Kwamishinoni 7 Sun Ajiye Aikinsu, An Shiga Ruɗani Kan Murabus Ɗin Shugaban Fadar Ma'aikatan Gwamna

Kwamishinoni 7 Sun Ajiye Aikinsu, An Shiga Ruɗani Kan Murabus Ɗin Shugaban Fadar Ma'aikatan Gwamna

  • A kalla kwamishinoni guda bakwai ne suka ajiye aikinsu daga fadar gwamnatin Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta.
  • Kwararan majiyoyi daga gwamnatin na Okowa sun ce shugaban fadar ma'aikatan gwamnan shima ya ajiye aikinsa amma da aka tuntube shi ya musanta hakan
  • Rahotanni sun nuna cewa akwai yiwuwar murabus din na kwamishinonin yana da nasaba da sabuwar dokar zabe da ta ce maus mukami su ajiye aiki kafin shiga takara

Delta, Asaba - A kalla kwamishinoni bakwai ne ciki har da shugaban fadar ma'aikatan gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ne suka yi murabus daga gwamnatin jihar, The Punch ta rahoto.

Baya da shugaban fadar ma'aikatan, Festus Agas, wanda ya karyata rahoton, sauran da suka yi murabus sun sun hada da Basil Ganagana, Evelyn Oboro, Julius Egebedi, Jonathan Ukodhiko, Christian Onoga, Ovie Oghoore da Chika Ossai.

Kwamishinoni 7 Sun Ajiye Aikinsu, An Shiga Ruɗani Kan Murabus Ɗin Shugaban Fadar Ma'aikatan Gwamna
An Shiga Ruɗani Kan Murabus Ɗin Shugaban Fadar Ma'aikatan Gwamna Okowa. Hoto: The Punch

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An gano cewa yin murabus dinsu ba zai rasa nasaba da sashi na 84 na dokar zabe na 2022 ba.

Dokar ta bukaci duk wani da ke da niyyar yin takarar zabe ko zama deleget a 2023 ya ajiye mukaminsa.

Amma, Agas, a ranar Juma'a ya ce bai riga ya ajiye aikinsa ba.

A makon da ta gabata, Okowa ya bada umurnin cewa duk wani da ke fadarsa da ke da niyyar yin takara ya yi ajiye aikinsa.

An rahoto cewa ana sirranta murabus din na Agas, duba da cewa an hange shi yana zuwa ofis daga ranar Litinin har zuwa yau Juma'a.

Majiyoyi daban-daban sun nuna Agas ya yi murabus

An gano cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar ya ajiye aikinsa a ranar Litinin.

Majiyoyi masu inganci daga gwamnatin Okowa, yayin tabbatar da batun murabus dinsa, sun ce Agas ya fara kwashe muhimman kayansa daga ofishinsa.

Kazalika, hadimin Okowa, Ossai Ovie Success, a wani wallafa da ya yi a Facebook, ranar Alhamis, ya tabbatar da murabus din Agas.

Ya rubuta cewa:

"Na ji dadin aiki da Rt Hon Festus Ovie Agas wanda yanzu-yanzu ya yi murabus a matsayin shugaban ma'aikatan fadar gwamnati a Asaba. Mun yi zama mai dadi a ofis. Rt Hon Ovie Agas ya kasance mahaifi nagari, shugaba mai saukin kai da kyauta."

An dade na jita-jitar cewa Agas ya samu amincewar Okowa na shiga takarar gwamna a zaben 2023.

Agas ya ce bai yi murabus ba

Amma da wakilin The Punch ya tuntube shi, Agas ya musanta cewa ya ajiye aikinsa.

"Ba gaskiya bane, ban ajiye aiki ba, a yanzu da muke magana, ina ofishi na," ya shaida wa The Punch.

2023: Zan iya shugabancin Najeriya amma dai ban matsu ba, Orji Kalu

A wani labarin, bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Uzor Kalu, ya ce duk da a shirye ya ke da ya yi kamfen kuma zai iya shugabantar kasar nan, amma bai matse ya ce ai zama shugaban Najeriya ba, Daily Trust ta ruwaito.

Kalu, tsohon gwamnan Jihar Abia, ya yi wannan bayanin ne a ranar Laraba yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a Majalisar Tarayya, washegarin da ya kai wa Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja.

A cewarsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, takarar shugaban kasa hukunci ne ‘yan Najeriya zasu yanke sannan ko wacce jam’iyya zata zabi bangaren da za ta bai wa damar tsayawa takara, musamman jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel