Da dumi-dumi: Fayemi ya yi watsi da batun goyon bayan yan takarar da Buhari ke so
- Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya yi watsi da batun goyon bayan duk yan takarar da shugaba Buhari ke so gabannin taron APC
- Fayemi ya ce duk wani mai neman mukamin shugabanci a jam'iyyar zai fito ne ya fafata a ranar Asabar mai zuwa
- Hakan na zuwa ne bayan rahoton cewa gwamnonin jam'iyyar mai mulki sun amince da goyon bayan zabin shugaban kasar
Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti ya karyata batun goyon bayan yan takarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lamunce mawa gabannin babban taron jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Daily Trust ta rahoto.
Da yake magana a taron tattaunawa kan manufofi da cibiyar ci gaban damokradiyya wato Centre for Democracy and Development (CDD), ta shirya a ranar Alhamis, 24 ga watan Maris, Fayemi ya karyata goyon bayan yan takarar da shugaban kasa yake goyon baya.
Furucin Fayemi zai ba mutane da dama mamaki domin yana daga cikin gwamnonin APC da suka tabbatar da tsarin cimma matsaya daya bayan ganawarsu da shugaba Buhari a daren ranar Laraba, 23 ga watan Maris.
Rikici ya dabaibaye jam’iyyar mai mulki kan zabin wadanda za su shugabanci jam’iyyar na gaba a matakin kasa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tun farko dai mun ji cewa goyon bayan Sanata Abdullahi Adamu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa ya haifar da rikici a jam’iyyar.
Amma daga cikin kokarin magance lamarin, Buhari ya gana da gwamnoni a fadar villa a ranar Laraba, 23 ga watan Maris, inda bayan nan aka ce sun cimma matsaya daya.
Daily Trust ta kuma reahoto cewa wani gwamna daga arewa ta yamma ya bayyana cewa ba a yi adawa ba lokacin da aka gabatar da batun tsayar da Adamu. Ya kuma ce an magance batun sakataren jam’iyyar na kasa.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron, shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya ce an cimma matsaya don cike mukaman NWC ta hanyar fahimtar juna.
Ya ce kungiyar gwamnonin na APC na goyon bayan dan takarar shugaban jam’iyyar da shugaba Buharin yake goyon baya koda dai ya ki ambatan sunan dan takarar.
Babu yadda gwamnonin APC suka iya, sun goyi bayan wanda Buhari ke so a zaben jam'iyya
A baya, mun kawo cewa a ranar Laraba, 23 ga watan Maris 2022, gwamnonin da suke mulki a karkashin jam’iyyar APC suka yi na’am da abin da shugaban kasa ya zo da shi.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa gwamnonin na jam’iyyar APC sun yarda su goyi bayan Sanata Abdullahi Adamu ya zama shugaban APC na kasa.
Tun tuni Muhammadu Buhari ya nuna cewa Abdullahi Adamu yake sha’awar ya rike jam’iyya. Wannan matakin ya nemi ya jawo sabani tsakanin ‘yan APC.
Asali: Legit.ng