Mu ne muka kashe kasar nan, ya kamata yanzu ina gidan kurkuku inji Tsohon Ambasada

Mu ne muka kashe kasar nan, ya kamata yanzu ina gidan kurkuku inji Tsohon Ambasada

  • Wani tsohon Minista da aka taba yi a kasar nan ya yi wa ‘yan siyasa kudin goro, ya ce sun cuci kasa
  • Ibrahim Musa Kazaure ya sa kan shi a cikin wadanda ya kamata a ce an daure su a gidan gyaran hali
  • Ambasada Ibrahim Musa Kazaure bai cire kan shi daga cikin wadanda suka jefa al’umma a ha’ula’i ba

Abuja - Daily Trust ta rahoto Ambasada Ibrahim Musa Kazaure yana mai tir da halin ‘yan siyasa. Kazaure ya ce 'yan siyasa ba su yi amfani da damar su ba.

Tsohon Ministan ayyukan ya yi Allah-wadai a game da irin shugabannin da aka rika samu tun da aka dawo tsarin mulkin farar hula, ya zarge su da kashe kasa.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban majalisar wakilan tarayyar da ya rika karbar albashin N15, 000 ya rasu

Ibrahim Musa Kazaure ya yi wannan zance ne a lokacin da aka yi hira da shi a gidan rediyon RFI. Kazaure ya koka a kan yadda malaman jami’a suke yajin-aiki.

Zargin da Ibrahim Musa Kazaure yake yi wa ‘yan siyasar ya shafi duk wadanda aka dama da su a gwamnati tun daga lokacin da sojoji suka mika mulki a 1999.

A cewar Ambasada Kazaure, ana tafka sata ta la-hau-la a gwamnatin Najeriya, yayin da aka bar talakawan da suka zabi shugabannin su na cikin wani irin hali.

Amb. Kazaure ya yi kudin goro

Kazaure wanda ya rike Jakadan Najeriya zuwa Saudi Arabia a shekarun baya, ya ce duk arzikin da Allah ya yi wa kasar nan, babu abin da yake tafiya a daidai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ambasada Kazaure
Ibrahim Musa Kazaure tare da Sule Lamido Hoto: @mansurahmed09
Asali: Twitter

“Ko ni da nake yi maka magana, abin da muka yi wa Najeriya, ya cancanci a daure mu.”

Kara karanta wannan

Jami'an DSS Sun Harbe Wani Soja Har Lahira a Jihar Legas

“Ina yawan cewa; Ni, Ibrahim Musa Kazaure, mun cuci Najeriya da talakawanta. In fada maku gaskiya, dukkanmu duk daya mu ke.”
“Abin da muka yi a lokacin da muka samu dama, ba shi ya dace mu yi ba, domin wasunmu sun samu dama, wasu kuma ba su samu ba.”
“Ba wannan gwamnatin kurum ba, dukkanmu babu abin da muka tabuka. Da a ce mun yi wani abin kwarai, da Najeriya ba haka ta ke ba.”

Ba a ci moriyar arzikin Najeriya ba

“Mu na da arziki da mutanen da za mu gyara, dubi abin da kananan kasashe su ka zama, yanzu don takaici sun zama wajen shakatawarmu.”

- Ibrahim Musa Kazaure

Tsohon Ambasadan ya ce yanzu ko an ba shi mukami kyauta ba zai karba ba, ya bada shawarar duk wani wanda ya saci kudin gwamnati, ya dawowa baitul-mali.

Ana zagin 'yan siyasa da banga

A makon nan ne DSS ta taso manyan ‘yan siyasar Kano a gaba, an kama shugabannin kananan hukumomi 2, ana kuma neman shugaban karamar hukumar Gwale.

Kara karanta wannan

Magana ta dawo baya: Gwamnati ta ce babu kudin da malaman jami'a masu yajin-aiki ke nema

Hukumar DSS ta yi wa Murtala Garo, AbdulSalam Abdulkarim Zaura, Baffa Dan’gundi da Alhassan Ado Doguwa tambayoyi a kan kashe-kashen da aka yi a taron APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel