El-Rufai: Idan Buhari Ya Matsa, Zan Yi Takarar Shugaban Ƙasa a 2023 Amma Ba Don Ina So Ba

El-Rufai: Idan Buhari Ya Matsa, Zan Yi Takarar Shugaban Ƙasa a 2023 Amma Ba Don Ina So Ba

  • Nasir El-Rufai, gwamnan Jihar Kaduna ya ce zai yi takarar shugabancin kasa a 2023 amma fa sai idan Shugaba Buhari ya matsa masa ya yi hakan
  • El-Rufai ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke bada amsa kan jita-jitar da ake yada wa na cewa zai yi takarar shugaban kasa tare da Rotimi Amaechi
  • Tsohon ministan na Abuja ya ce a ra'ayinsa baya son neman wata kujera kamar yadda ya sha nanatawa domin shekaru sun fara masa yawa don haka zai rika bawa kasa gudunmawa ta wani hanyar

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce bashi da niyyar neman wata kujera a babban zaben 2023 amma zai iya canja ra'ayinsa idan Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci hakan, rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Akwai Yiwuwar Mace Ce Za Ta Zama Gwamnan Kaduna A 2023

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin martani kan jita-jitar da ake yada wa cewa shi ne zai yi takarar mataimakin shugaban kasa tare da gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi na zabe mai zuwa.

El-Rufai: Idan Buhari Ya Matsa, Zan Iya Yin Takarar Shugaban Ƙasa a 2023 Amm Ba Don Ina So Ba
El-Rufai: Ba Domin Ina So Ba, Zan Iya Yin Takarar Shugaban Ƙasa a 2023 Idan Buhari Ya Matsa Min. Hoto: Gwamnan Jihar Kaduna
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Na sha nanatawa cewa ba zan nemi wata kujerar siyasa ba. Bana neman komai," ya ce a shirin Politics Today na Channels Television.
"Idan Gwamna Rotimi Amaechi yana sha'awar neman wata kujera, yana da damar yin hakan. Amma ni bana neman komai kuma ba tare da shi zan yi takara ba."

Ba ni da niyyar takara amma idan Buhari ya matsa, zan yi domin ina ganin girmansa, El-Rufai

Da aka masa tambaya shin ko Buhari zai iya sa shi ya sauya ra'ayinsa, El-Rufai ya bada amsa da cewa:

"Wannan wani zance ne na daban. Zan masa bayanin dalilin da yasa na ke ganin ba abu mai kyau bane, amma idan ya matsa, zan yi. Amma na gaji.

Kara karanta wannan

Buhari bai lamunce mun don darewa kujerar shugaban APC na kasa ba – Sanata Abdullahi Adamu

"Gabobi na sun gaji domin bana wasa da aiki na. Tsawon shekaru bakwai ko takwas. Na kasance ina aiki ba dare ba rana kuma ga shi na fara tsufa.
"Zan cika shekaru 63 a shekara mai zuwa. Don haka, zan fi son in nemi wasu hanyoyin da zan iya bawa kasa ta gudunmawa. Ban yi niyyar takarar gwamna ba amma idan Shugaban kasa ya matsa sai nayi kuma ina ganin girmansa da zai sa in yi koda bana so."

Ina kyautata zaton APC za ta lashe zabe mai zuwa, El-Rufai

Baya ga batun takarar shugaban kasa, El-Rufai ya kuma kyautata zato cewa jam'iyyarsa ta All Progressives Congress (APC) ita ce za ta lashe babban zabe mai zuwa.

Ya ce ba duka abin da yan Najeriya ke tsammani jam'iyyarsu ta aikata ta yi ba amma dai idan aka yi nazari mai zurfi, gara jam'iyyarsu din a cewar tsohon ministan na birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Da ace EFCC na aikinta yadda ya kamata, da wasu masu neman kujerar Buhari suna kurkuku - Obasanjo

Babagana Zulum: Ba ni da niyyar fito wa takara a zaɓen 2023

A wani labarin, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya ce baya sa ran neman wata mukamin siyasa a shekarar 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Akwai rade-radin cewa gwamnan yana neman yin takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a Najeriya.

Amma, da ya ke magana wurin taron tattaunawa karo na 19 da Daily Trust ta shirya a ranar Alhamis a Abuja, ya ce bai taba fatan zai zama gwamna ba ma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel