El-Rufai: Akwai Yiwuwar Mace Ce Za Ta Zama Gwamnan Kaduna A 2023

El-Rufai: Akwai Yiwuwar Mace Ce Za Ta Zama Gwamnan Kaduna A 2023

  • Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce ta yuwu mace ce zata maye gurbinsa idan lokacin saukar sa ya yi a 2023
  • Ya yi wannan bayani ne a ranar Talata inda yace ganin yadda kusan rabin jama’an jihar mata ne, hakan zai iya tabbata
  • Ya bayar da misali akan yadda ya ba mata mukaman kwamishinoni a manyan ma’aikatun jiharsa wanda a cewarsa sun yi aiki fiye da maza

Kaduna - Gwamna Nasir El-Rufai ya ce mace za ta iya zama gwamnan Jihar Kaduna a 2023 musamman idan aka yi la’akari da yadda mata da dama suke da karfi a jihar, Premium Times ta ruwaito.

Wannan ne karon El-Rufai na biyu a ofishinsa wanda zai gama a shekarar 2023. Kuma mataimakiyar sa Hadiza Balarabe, mace ce.

Kara karanta wannan

Wani hanin: Bayan shekaru 12 tana dako, Allah ya azurta mata da haihuwar 'ya'ya hudu nan take

El-Rufai: Akwai Yiwuwar Mace Ce Za Ta Zama Gwamnan Kaduna A 2023
El-Rufai: Akwai Yiwuwar Mace Ta Gaji Kujera Ta 2023. Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Talata, gwamnan ya ce akwai yuwuwa kaso 50% na zaben mace ta lashe zaben gwamna saboda mata su ne rabin yawan jihar.

El-Rufai ya ce gwamnatinsa zata ci gaba da ba wa mata dama, inda ya kula da cewa ya ba mata mukaman kwamishinoni a manyan ma’aikatun jiharsa.

Rabin yawan mutanen jihar mata da matasa ne, El-Rufai

Kamar yadda Premium Times ta bayyana, El-Rufai ya ce:

“Ba za ka iya share rabin yawan mutanen ka ba; yin hakan kamar tafi ne da hannu daya. Kaso 50% na mutanen mu mata ne da matasa.
“Muna ganin ba mata damar a dama da su zai kawo ci gaba, kuma zasu yi aiki fiye da mazan.
“Mun yi kokarin gano mata masu kwazo kuma mun ba su dama inda suka nuna mana cewa zasu iya, ba su bamu kunya ba. Suna matukar kawo ci gaba a Jihar Kaduna.”

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsohon dan wasan kwallon Najeriya ya yanki jiki ya fadi matacce a Jos

El-Rufai ya bukaci sauran yankuna su kwafi irin salon sa na ba mata dama

Ina tunanin zai dace ace sauran yankunan kasar nan sun ba mata da matasa dama don ciyar da kasar nan gaba.

Gwamnan ya ce jihar za ta samar da shugabannin da suka dace wadanda zasu bunkasa ta.

Ya bukaci mutanen jihar da su taya shi addu’o’i don samar da jagora wanda zai kawo ci gaba mai yawa.

Ya ce samar wa mutanen Jihar Kaduna mace ko namiji mai kwazo a matsayin shugaba zai tallafa wa jihar ya kuma kawo gyara ga kura-kuran da ya yi tare da ciyar da jihar gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel