Tsohon Sanatan Kaduna ya fice daga PDP, ana kishin-kishin Kwankwaso zai ja shi NNPP
- Suleiman Othman Hunkuyi ya rubuta takarda, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar adawa ta PDP
- Sakataren jam’iyya ya ce ba wannan ne karon farko da Suleiman Othman Hunkuyi ya bar PDP ba
- Sanata Hunkuyi ya wakilci mutanen Kaduna ta Arewa a majalisar dattawa tsakanin 2015 da 2019
Kaduna - Sanata Suleiman Othman Hunkuyi wanda ya wakilci Arewacin jihar Kaduna a majalisar dattawan kasar nan, ya fita daga jam’iyyar adawa.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Alhamis 3 ga watan Maris 2022 cewa Suleiman Othman Hunkuyi ya bada sanarwar barin jam’iyyar PDP.
Wannan ne karo na biyu da ‘dan siyasar zai sauya-sheka a cikin kusan shekaru hudu. Gabanin zaben 2019 ne Hunkuyi ya shiga PDP daga APC mai mulki.
Kafin shigarsa APC, Sanata Suleiman Hunkuyi yana cikin jagororin jam’iyyar PDP a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan
Abin da PDP za tayi kafin tayi nasara a zabe - Gwamna Tambuwal ya bada lakanin 2023
Daily Post ta ce tsohon ‘dan majalisar ya rubuta takarda a ranar 25 ga watan Fubrairu, ya na mai sanar da shugabannin PDP wannan matakin da ya dauka.

Asali: Twitter
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kamar yadda Legit.ng Hausa ta samu labari, Hunkuyi ya aika wannan wasika ga shugaban PDP a mazabar Hunkuyi a karamar hukumar Kudan, jihar Kaduna.
Hunkuyi ya sanar da shugaban PDP na Hunkuyi cewa ya tashi daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar daga wannan rana ta Juma’a da ya sa hannu a takardar ta murabus.
Babu abin da zai canza a PDP
Sakataren jam’iyyar PDP na jihar Kaduna, Ibrahim Wosono ya tabbatarwa manema labarai cewa sun karbi takardar da Sanata Hunkuyi ya aikawa mazabarsa.
Ibrahim Wosono ya ce ba wannan ne karon farko da Hunkuyi ya bar PDP ba, don haka suka ce tashinsa ba zai canza komai ba, su na masu yi masa fatan alheri.

Kara karanta wannan
Shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu ya tsokano fushin Jami’an DSS da kalaman da ya yi
Ina Hunkuyi ya sa gaba?
Sanata Suleiman Hunkuyi bai bayyana jam’iyyar da ya koma ba zuwa yanzu. Amma rahotanni na nuna cewa babu mamaki ya yi rajista da jam’iyyar nan ta NNPP.
A halin yanzu ana rade-radin cewa Rabiu Kwankwaso da wasu mabiyansa za su koma NNPP. Hunkuyi yana cikin wadanda suke tare da Sanata Kwankwaso.
Kwankwaso zai bar PDP
Yanzu nan mu ke jin labari cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya sa ranar da zai fice daga babbar jam'iyyar hamayya ta PDP.
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa kafin karshen watan nan na Maris zai sauya-sheka. Akwai yiwuwar Kwankwaso ya shiga jirgin NNPP.
Asali: Legit.ng