Yadda Shugaba Buhari ya ba babban ‘dan adawarsa kunya da sa hannu a dokar gyaran zabe

Yadda Shugaba Buhari ya ba babban ‘dan adawarsa kunya da sa hannu a dokar gyaran zabe

  • Fitaccen dan siyasar nan, Buba Galadima ya taba cewa ba a za a taba sa hannu a kudirin zabe ba
  • Watanni hudu da yin maganar Injiniya Buba Galadima, Muhammadu Buhari ya amince da dokar
  • Jama’a na tunawa Galadima maganar da ya yi na cewa a datse masa kai idan kudirin ya zama doka

Abuja - Kwanakin baya aka rahoto Injiniya Buba Galadima yana cewa ya san babu abin da zai sa Muhammadu Buhari ya amince da kudirin gyaran zabe.

Abin har ta kai BBC ta rahoto Buba Galadima yana cewa idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannunsa a kudirin zabe, ya yarda a fille masa kai.

Injiniya Galadima ya shaidawa manema labarai wannan a wata tattaunawa a Disamban 2021. Watanni hudu da yin haka, sai aka ji an sa hannu a kudirin.

Kara karanta wannan

Dokar zabe: Yadda Gwamnatin Jonathan ta so bankara doka domin hana Buhari mulki

Hakan ta sa Legit.ng Hausa ta tunawa Galadima maganganun da ya yi, yana mai cewa Buhari yana tsoron kudirin ne domin ya san APC ba za ta iya cin zabe ba.

Tsohon sakataren na jam’iyyar CPC kuma abokin tafiyar siyasar Buhari a wancan lokaci, yana ganin tsoron kato-bayan-kato ya sa aka ki amincewa da kudirin.

Shugaba Buhari
Shugaba Buhari da Buba Galadima Hoto: koko.ng
Asali: UGC

A fille mani kai - Buba Galadima

“Na amince a fille min kai idan har Buhari ya sa hannu kan wannan kudurin dokar."

- Buba Galadima

Labari ya canza

Sa hannun da shugaban Najeriyar ya yi a kan wannan kudiri da zai gyara sha’anin zabe a kasar nan ya zama tamkar kunyata Buba Galadima da ire-irensa a kasar.

Sai dai za a iya cewa kudirin bai zama doka ba har sai da aka cire sharadin zaben kato-bayan-kato.

Kara karanta wannan

Buhari: Ba Zan Zarce 2023 Ba, Na Yi Rantsuwa Da Kur'ani

Martanin Buba Galadima

A wata hira da ya yi da jaridar Punch, Galadima ya bayyana cewa har yanzu tamkar ba a sa hannu a kan kudirin gyaran zaben ba domin akwai sauran aiki.

‘Dan siyasar ya ce Buhari ya sa hannu a kudirin ne kurum saboda matsin lambar kungiyoyi da ‘yan jaridu, kuma a karshe a boye za a cire sharudan da ba a so.

Galadima ya misalta sa hannun da aka yi da 419, ya ce duk da ana gani kamar kudirin ya zama doka a tsarin mulkin kasa, za a janye wasu ka’idoji daga cikinsa.

PDP vs DSS

Dazu ku ka ji labari cewa shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu ya tsokano fushin Jami’an DSS da kalaman da ya yi, yana zargin hukumar tsaron da nuna son kai.

Mai magana da yawun DSS na kasa, Peter Afunanya ya fitar da jawabi yana mai raddi, ya ce burinsu shi ne tsare al’ummar kasar, ba zaluntar Bayin Allah ba.

Kara karanta wannan

Duk shugaban da ya rantse da AlQur'ani kada ya kuskurar yaci amana, Shugaba Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel