Ya Ci Amanarsa: Jigon PDP Ya Bayyana Alaƙa Da Ke Tsakanin Buhari Da Saraki a 2015

Ya Ci Amanarsa: Jigon PDP Ya Bayyana Alaƙa Da Ke Tsakanin Buhari Da Saraki a 2015

  • Alhaji Kawu Baraje, tsohon shugaban tsagi na jam'iyyar PDP na kasa ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya ci amanar Bukola Saraki
  • Baraje ya ce Saraki ya yi amfani da kudinsa, lokacinsa da karfinsa don ganin Buhari ya zama shugaban kasa amma bayan ya yi nasara sai ya rika masa bita da kulli
  • Baraje ya kuma bayyana cewa jam'iyyar ta PDP ba za ta karaya ba sai ta kwato wa mataimakin gwamnan Jihar Zamfara, Mahdi Aliyu kujerarsa

Tsohon shugaban tsagi na jam'iyyar PDP na kasa, Alhaji Kawu Baraje, a ranar Talata ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya ci amanar tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki jim kadan bayan shi (Buhari) ya shiga ofis.

Da ya ke magana yayin taron shugabannin PDP a Gusau, Jihar Zamfara, Baraje ya ce gwamnatin Shugaba Buhari ta yi karar Saraki har sau biyar a kotu amma shi (Sarakin) ya yi nasara, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

2023: Sarkin Yarbawa ya yi magana kan Osinbajo, ya ce masoya su daina matsa masa

Buhari Ya Ci Amanar Saraki Bayan Ya Lashe Zaɓe, in Ji Kawu Baraje
Baraje: Buhari Ya Ci Amanar Saraki Bayan Ya Lashe Zaɓe
Asali: Twitter

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bukola ya yi amfani da kudinsa, lokacinsa da karfinsa domin tabbatar da cewa Shugaba Buhari ya lashe zaben shugaban kasa na 2015.
"Amma, bayan ya lashe zaben, Shugaba Buhari ya rika maka Saraki a kotu bisa zargi marasa tushe."

Baraje ya ce za a kwato wa Mahdi Aliyu Gusau hakkinsa

Ya bawa shugabannin PDP na Jihar Zamfara tabbacin cewa tsige mataimakin gwamnan jihar, Barista Mahdi Aliyu Gusau, da aka yi ba bisa ka'ida ba ba zai dore ba kuma za a mayar da shi kujerarsa.

Daily Trust ta rahoto cewa ya ce Saraki ne zai zama shugaban Najeriya na gaba, ya kara da cewa zai yi nasara ne saboda juriya, aiki tukuru, rashin karaya na mambobin PDP a kasar.

"Bita da kullli da aka yi wa mambobin PDP a Zamfara da sauran jihohi ba zai karya mana gwiwa mu dena kokarin kwato hakkin mu ba wannan shi ke tada wa gwamnatin APC hankali," in ji Baraje.

Kara karanta wannan

Ministoci da Shugabannin Gwamnatin da ke daf da asarar kujerunsu a sabuwar dokar zabe

A jawabinsa, shugaban PDP na Zamfara, Kwanel Bala Mande (mai ritaya) ya ce Saraki ya yi shugabanci na gari kuma zaiyi aiki tukuru don ganin jam'iyyar ta yi nasara a dukkan matakai.

2023: Zan iya shugabancin Najeriya amma dai ban matsu ba, Orji Kalu

A wani labarin, bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Uzor Kalu, ya ce duk da a shirye ya ke da ya yi kamfen kuma zai iya shugabantar kasar nan, amma bai matse ya ce ai zama shugaban Najeriya ba, Daily Trust ta ruwaito.

Kalu, tsohon gwamnan Jihar Abia, ya yi wannan bayanin ne a ranar Laraba yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a Majalisar Tarayya, washegarin da ya kai wa Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja.

A cewarsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, takarar shugaban kasa hukunci ne ‘yan Najeriya zasu yanke sannan ko wacce jam’iyya zata zabi bangaren da za ta bai wa damar tsayawa takara, musamman jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel