Rikici: APC da Buhari sun nemi a yi watsi da karar da ke neman tsige Buhari a daura Atiku

Rikici: APC da Buhari sun nemi a yi watsi da karar da ke neman tsige Buhari a daura Atiku

  • Kungiyar farar hula ta Civil Society Observatory for Constitutional and Legal Compliance (CSOCLC) ba ta shirya ja da baya a kokarinta na ganin an tsige Buhari daga mukaminsa
  • Kungiyar CSOCLC, bayan rashin nasara a babbar kotu, ta garzaya kotun daukaka kara da ke Abuja inda ta nemi a sauke Buhari tare da ayyana Atiku a matsayin shugaban kasa
  • Shugaba Buhari da jam’iyyarsa ta APC ta bakin lauyoyinsu sun bukaci kotun da ta yi watsi da karar, inda suka ce kungiyar ta kasa tabbatar da zargin da take yi a babbar kotun

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci kotun daukaka kara da ke Abuja ta yi watsi da karar da aka shigar na neman soke zabensa tare da rantsar da tsohon mataimakin shugaban kasa Abubakar Atiku a matsayin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Atiku ya samu gagarumin goyon baya daga wata kungiyar Inyamurai

Wata kungiyar farar hula mai suna Civil Society Observatory for Constitutional and Legal Compliance (CSOCLC) ne ta shigar da kara, inda ta bayyana cewa takardar rantsuwar kotu da shugaba Buhari ya gabatar a zaben 2019 ta karya ce, inji rahoton Daily Trust.

Babban kotu kan batun tsige Buhari a daura Atiku
Rikici: APC da Buhari sun nemi a yi watsi da karar da ke neman tsige Buhari a daura Atiku | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Twitter

CSO, ta bakin lauyanta, Nnamdi Ahaiwe Esq., ta bayyana cewa takardar rantsuwar kotu da shugaba Buhari ya yi a ranar 24 ga watan Nuwamba, 2014, a babban kotun tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja cewa:

“Dukkan takardun shaidarsa na karatu kamar yadda ya cika a cikin fom dinsa na neman takarar shugaban kasa, APC/001/ 2015 a halin yanzu suna tare da Sakataren Hukumar Soja, cewa a lokacin rantsuwar karya ce."

Kungiyar ta CSO ta kuma bayyana cewa babu wata kungiya, cibiya, hukuma ko sashe da aka fi sani da suna ‘Military Board’ da ake da ita a Najeriya a daidai a ranar 24 ga watan Nuwamba 2014 lokacin da Buhari ya yi rantsuwar a babban kotun babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: APC ta tabbatar da ranar gudanar da babban taronta na kasa, 26 ga watan Fabrairu

Kungiyar ta nemi kotu ta rusa zaben Buhari, tare da karbe takardar komawarsa mulki hakazalika ta umarci INEC ta mika takardar shiga ofis ga Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019.

Martanin Buhari da jam'iyar APC

A martanin da suka mayar, shugaba Buhari da jam’iyyarsa ta APC, sun gabatar da cewa, gazawar kungiyar CSO wajen tabbatar da tuhumar da take yi a babbar kotu, ya nuna gazawarta.

Sun bayyana cewa Kotun Koli ta warware batun daukaka kara tsakanin Atiku da wani, tsakaninsa da INEC da dai sauransu, tare da tabbatar da cewa a karkashin doka, kotun daukaka kara ta tsaya kan hukuncin da kotun koli ta yanke tun farko.

Legit.ng ta tattaro cewa jam’iyyar APC da shugaba Buhari sun gabatar da bayanai a cikin wata takaitacciyar hujjar da suka cike a ranar 31 ga watan Junairu, 2022, suna kalubalantar daukaka karar da CSO ta shigar.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Okorocha ya gana da Buhari kan kudirinsa na son zama magajinsa

An dage shari'ar

A halin da ake ciki kuma, a zaman da aka ci gaba da yi a ranar Laraba, 9 ga watan Fabrairu, lauyoyi biyu, Oluwole Afolabi da F. O. Amedu, sun wakilci jam’iyyar APC da shugaba Buhari inda suka ce an yi musu cikakken bayani.

Sakamakon haka, kwamitin mutum uku a karkashin jagorancin Mai shari’a Haruna Tsamani ya dage karar zuwa ranar Laraba 18 ga watan Mayu domin samun damar daidaita batun wakilcin.

A wani labarin, tsohon sakataren jam'iyyar Labour Party (LP), Kayode Ajulo, yace mafi yawan gwamnonin PDP da APC na goyon bayan mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya gaji Buhari a 2023.

Da yake jawabi yayin fira a cikin shirin Channels TV 'Siyasa a yau' Ajulo ya ce Osinbajo ya yi abin a zo a gani cikin shekaru bakwai da suka wuce, wanda ya dace a bashi dama ya gaji Uban gidansa.

Kara karanta wannan

Zargin siyasa: Majalisa ta tabbatar da nadin kwamishinan INEC da ake zargin yar APC ce

A cewarsa, ba bu wanda ya samu damar gano wani kuskuren Osinbajo, dan haka ya kamata a ba shi dama ya zama shugaban kasa na gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel