2023: An bayyana mutumin da gwamnonin PDP da APC ke son ya gaji kujerar Buhari

2023: An bayyana mutumin da gwamnonin PDP da APC ke son ya gaji kujerar Buhari

  • Fitaccen ɗan siyasa kuma tsohon Sakataren LP na ƙasa, Kayode Ajulo, yace mataimakin shugaban ƙasa ya dace ya gaji Buhari a 2023
  • A cewarsa, mafi yawan gwamonin manyan jam'iyyun siyasa APC da PDP na goyon bayan Farfesa Yemi Osinbajo
  • Ya ce tsawon lokaci Osinbajo na rike da mataimakin shugaban ƙasa kuma ya taka rawar gani da ya dace a ba shi takara

Abuja - Tsohon sakataren jam'iyyar Labour Party (LP), Kayode Ajulo, yace mafi yawan gwamnonin PDP da APC na goyon bayan mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, ya gaji Buhari a 2023.

Da yake jawabi yayin fira a cikin shirin Channels TV 'Siyasa a yau' Ajulo ya ce Osinbajo ya yi abin a zo a gani cikin shekaru bakwai da suka wuce, wanda ya dace a bashi dama ya gaji Uban gidansa.

Kara karanta wannan

2023: Dalilai 2 da suka sa Farfesa Osinbajo ba zai yi takara da Bola Tinubu ba - Jigon APC

Farfesa Yemi Osinbajo
2023: An bayyana mutumin da gwamnonin PDP da APC ke son ya gaji kujerar Buhari Hoto: Professor Yemi Osinbajo
Asali: Facebook

A cewarsa, ba bu wanda ya samu damar gano wani kuskuren Osinbajo, dan haƙa ya kamata a ba shi dama ya zama shugaban ƙasa na gaba.

Ya kuma yi kira ga jam''iyyar All Progressive Congress (APC) ta duba yuwuwar miƙa wa mataimakin shugaban ƙasa tikitin takara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Fitaccen ɗan siyasan yace matukar APC dagaske take tana son ta zarce da mulkin Najeriya, to mutumin da zai iya kawo mata nasara shi ne Farfesa Osinbajo.

Yace:

"Muna bukatar banbance ofishin mataimakin shugaban ƙasa, da halayen Farfesa Yemi Osinbajo, domin a halin yanzun takararsa ba ta bukatar tattaunawa."
"Zan iya faɗa cikin yaƙini cewa waɗan da ke fadar shugaban ƙasa suna jin abin da na faɗa. Yana da yancin ƙin amince wa da farko, musaman a matsayinsa na yanzu."
"Tun da har ya iya zama mataimaki na tsawon lokaci haka, ya kamata ya zama shugaban ƙasa na gaba. Ina fatan jagororin jam'iyya su gane haka."

Kara karanta wannan

Yemi Osinbajo ya fadakar da jama’a a kan ‘yan siyasan da za su nesanta a zaben 2023

Shin Osinbajo zai yi takara da Tinubu?

Mista Ajulo ya yi watsi da ikirarin jigon APC, Daniel Bwala, cewa Farfesa Osinbajo ba zai nemi takarar shugaban ƙasa a 2023 ba.

Yayin da wa'adin mulkin shugaban ƙasa ke kara matso wa, yan Najeriya na cigaba da fafutukar ganin wanda zai maye gurbin kujerar a zaɓe mai zuwa.

A wani labarin kuma Uwar gidan shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari ta kai ziyarar ta'aziyya jihar Kano, tace wajibi a yi adalci

Uwar gidan shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari ta kai ziyarar ta'aziyyar rasuwar Sheikh Ahmad Bamba da Hanifa Abubakar.

Aisha Buhari ta yi bayani mai ratsa zuciya game da Hanifa, inda tace ita ma uwa ce kuma tana da jikoki a makarantar Firamare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel