Kwankwaso: Na ki goyon bayan Tofa, Rimi, Buhari na zabi Abiola, Obasanjo da Jonathan

Kwankwaso: Na ki goyon bayan Tofa, Rimi, Buhari na zabi Abiola, Obasanjo da Jonathan

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya yi watsi da zargin da ake yi masa na nuna kabilanci a tafiyar siyasarsa
  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana yadda ya rika marawa ‘yan siyasar Kudu baya a zabe
  • Tsohon Gwamnan ya goyi bayan na su ne a maimakon ‘yan siyasar da suka fito daga yankin Arewa

FCT, Abuja - A wata tattaunawa da ya yi da Africa Courier International Magazine, Rabiu Musa Kwankwaso ya wanke kan shi daga zargin bangaranci.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tabbatar da cewa shi ba mutum ba ne da yake duba kabila ko yankin da mutum ya fito kafin ya yi tafiya da shi a siyasa.

Sai dai ma akasin haka, inda ya ce ya taimakawa ‘yan siyasar da suka fito daga yankin kudancin Najeriya da gudumuwa wajen ganin sun dare kan mulki.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Sanata Rabiu Kwankwaso ya shiga tsaka mai wuya

Wani mai goyon bayan Darikar Kwankwasiyya a Najeriya, Hasan Tukur ya tsakuro wani bangare na wannan hira da aka yi, ya wallafa a shafinsa na Twitter.

A bidiyon, za a ji Kwankwaso yana bada labarin yadda suka ba Olusegun Obasanjo goyon-baya a zaben fitar da gwani na shugaban kasa a jam’iyyar PDP a 1999.

A wancan lokaci tsohon gwamnan Kano, Alhajo Abubakar Rimi ya na neman ya yi takarar shugaban kasa, amma Cif Obasanjo ya samu galaba a kan shi.

Abin da Kwankwaso ya fada

“Tarihi ya maimaita kan shi a 1999, a lokacin na zama zababben gwamnan Kano. Mu ka je Jos domin zaben ‘dan takarar shugaban kasa.”
“Idan ba ka manta ba a lokacin, Muhammad Abubakar Rimi, jagoranmu daga Kano ya na takara, mu ka je mu ka ce masa dole ne ya janye.”

Kara karanta wannan

Mutanen Twitter sun ba PDP shawarar ta tsaida Peter Obi/Kwankwaso a zaben 2023

“Kai, na tattara duka masu shiga zaben fito da ‘dan takara a lokacin, mu ka wuce Kaduna kafin zaben fitar da gwani tare da wasu jagorori.”
“Mu ka samu jirgin sama har da Obasanjo, mu ka wuce har garin Jos, mu ka boye a wasu wurare domin mu marawa Obasanjo baya.”
“A lokacin mun yi imani cewa Obasanjo ne ya fi cancanta a cikin masu neman shugaban kasa.”

- Rabiu Kwankwaso

Kwankwaso
Rabiu Musa Kwankwaso da Dave Umahi ana gaisawa Hoto: mohd.saifullahi.9
Asali: Facebook

Mun yi Jonathan a 2011

“Za a ga yadda mutane suka yi aiki ba tare da la’akari da ra’ayin addini ko kabilanci ba. Ko a 2011, mun marawa Jonathan baya, ya ci zabe.”
“Kuma za ku tuna a zaben 1999, mutanen Kudu maso yamma ba su son Obasanjo, ya sha kashi a jiharsa, amma ‘Yan Arewa suka zabe shi.”

Zaben 1992

Haka aka yi ko a zaben shugaban kasa da aka yi a Yunin 1992, Kwankwaso su na cikin masu goyon bayan MKO Abiola a kan mutumin jihar Kano, Bashir Tofa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Likitan Bello Turji da ke masa jinya da kawo masa kwaya ya shiga hannu

Abin da mutane ba su sani ba shi ne, a inda Alhaji Tofa ya kada kuri’arsa, a nan akwatin Kwankwaso yake, kuma SDP ta doke NRC a Gandun Albasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel