Saura kiris wasu 'yan siyasar Najeriya su zama araha gama-gari, Shehu Sani ya fadi dalili

Saura kiris wasu 'yan siyasar Najeriya su zama araha gama-gari, Shehu Sani ya fadi dalili

  • Ko shakka babu da yawa daga cikin manyan ‘yan siyasar Najeriya da ke kan madafun iko a yanzu za su rasa kujerunsu a zaben 2023
  • A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 23 ga watan Janairu, tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana wasu maganganu akai
  • Sani ya ce bayan shan kayen da za su yi, yawancin ‘yan siyasar za a gansu ba tare da jami’an tsaro da mataimakansu da ke zagaye da su a yanzu ba

A cewar Shehu Sani, tsohon sanata daga jihar Kaduna, zaben 2023 zai sauya makomar wasu ‘yan siyasar Najeriya da dama.

Tsohon Sanatan ya bayyana cewa galibin mutanen da suke daukar kansu a matsayin alloli saboda karfin da suke dashi na mulki, bayan sauka daga mulkin za su rasa duk wata kariya da suke takama da ita.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello ga yan Najeriya: Ba zan ci amanarku ba idan kuka zabe ni shugaban kasa a 2023

Sanata Shehu Sani ya bayyana makomai 'yan siyasa
Saura kiris wasu 'yan siyasar Najeriya su zama araha gama-gari, Shehu Sani ya fadi dalili | Hoto: Shehu Sani
Asali: Twitter

Sani wanda ya fadi haka a Facebook a ranar Lahadi, 23 ga Janairu, ya yi hasashen cewa, irin wadannan ake ganin sun fi karfin kowa kuma ba za a taba taba su ba saboda isa da yawan jami'ai za su zama araha a cikin al'umma.

Ya bayyana cewa a karshe wadannan ‘yan siyasar za su rika gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum kamar sauran ‘yan kasa da ke nesa da dandana zakin mulki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

“A wasu watanni masu zuwa, mutanen da suke jin kansu kamar alloli a yau za su zama mutane gama-gari da za ku hadu da su a tashoshin jirgin kasa, filayen jirgin sama, masallatai, da coci.
“Mataimakansu, 'yan koronsu, da wadanda ke zagaye dasu za su barsu. Za su koma tafiya ba tare da tarin jami’an tsaron da ke kewaye da su ba.

Kara karanta wannan

Takarar shugaban kasa a 2023: Babatu 3 da Tinubu ya yi da ka iya sa ya fadi a 2023

“Wayoyinsu ba za su kara zama bizi ba kuma za su fara kiran wayan da basu dauka ba, za a iya samun su cikin sauki.
"Za su hadu da wadanda suka kyamata ko suka kuntatawa. Ba za su iya ba da doka ko umarni ba, sai dai nemo ko roko, baza su sami kariya ba, kuma za su lura da maganganunsu da matakansu, za su girbi abin da suka shuka."

Shugaban kasa a 2023: Tinubu na ci gaba da zawarci, ya ziyarci babban jigo na APC

A wani labarin, Babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ziyarci shugaban kwamitin ayyuka na majalisar dattawa, Sanata Sani Musa (APC Neja).

Ziyarar Tinubu na zuwa ne kwanaki uku bayan Gwamna Sani Bello na jihar Neja ya lamunce ma kudirinsa na neman takarar shugaban kasa.

Sanata Musa na daya daga cikin manyan yan takara da ke neman takarar kujerar shugabancin jam'iyyar APC na kasa a babban taron jam'iyyar mai zuwa.

Kara karanta wannan

2023: Tsohuwar Sanata ta aika saƙo mai tada hankali ga Tinubu, Osinbajo, Atiku da sauran ƴan takara

Asali: Legit.ng

Online view pixel