2023: Tsohuwar Sanata ta aika saƙo mai tada hankali ga Tinubu, Osinbajo, Atiku da sauran ƴan takara

2023: Tsohuwar Sanata ta aika saƙo mai tada hankali ga Tinubu, Osinbajo, Atiku da sauran ƴan takara

  • ‘Yan takaran da suke shirin maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2023 sun samu wani sako daga Florence Ita-Giwa a ranar Laraba 19 ga watan Janairu
  • Tsohuwar sanatan ta yi kira ga mata akan kada su kuskura su zabi wani dan takarar da ba mace ya tsayar a matsayin mataimakiyarsa ba
  • A cewar Ita-Giwa, lokaci ya yi da matan Najeriya za su mike tsaye don kwatar wa kawunansu hakki da katinan zaben su don su samu gurbi a siyasar kasar nan

FCT, Abuja - An tura wani sako na musamman ga matan Najeriya akan zaben shugaban kasa na shekarar 2023 da ke karatowa wanda ‘yan siyasa da dama suka nuna ra’ayin su akan tsayawa takara.

Kara karanta wannan

Damfarar N299.86m: Kotu na neman wani tsohon dan takarar gwamnan Zamfara

Sakon na jan hankali ne ga duk matan da ke kasar nan akan su mike tsaye don yakar duk wani dan siyasar da bai tsayar da mace a matsayin mataimakiyarsa ba a zabe mai zuwa, The Cable ta ruwaito.

2023: Tsohuwar Sanata ta aika saƙo mai tada hankali ga Tinubu, Osinbajo, Atiku da sauran ƴan takara
Tsohuwar Sanata ta ce kada mata su zabi duk wani dan takarar da bai tsayar da mace matsayin mataimakiyarsa ba a 2023. Hoto: (Ahmed Bola Tinubu, Prof. Yemi Osinbajo, Atiku Abubakar)
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan shawara ce daga Florence Ita-Giwa, tsohuwar sanata wacce ta bayar da ita ranar taron matan jam’iyyar APC da aka yi a Abuja ranar Laraba, 19 ga watan Janairu.

Ita-Giwa ta ba mata shawarar yadda zasu tsaya tsayin-daka ta hanyar amfani da katin zabensu wurin ganin sun sama wa mata gurbin shugabanci a kasar nan, The Cable ta ruwaito.

A cewarta, yanzu haka matan Najeriya suna shirin mulkar kasar nan daga mukamai daban-daban kuma hakan ba zai yuwu ba har sai an hada kai.

Kara karanta wannan

Babbar magan: Gwamna ya sanya hannu ya doka mai tsauri ta hana kiwo a fili

A kalamanta:

“Ya kamata mu nuna musu muna son mata su zama mataimakan gwamnoni. Saboda me baza mu yi hakan ba... a kasar nan yanzu haka, akwai mata masu kwazo, kaifin tunani da ilimin da zasu iya tsayawa akan mukamai.
“Ina ganin lokaci ya yi da mata zasu ce ba za su zabi duk wani dan takarar shugaban kasa ba matsawar bai tsayar da mace a matsayin mataimakiyarsa ba.
“Hakan ne abinda zamu yi don mu taimaki ‘yan bayan mu. Lokaci ya yi da mace zata zama mataimakiyar shugaban kasar Najeriya.”

2023: Manya masu son satar dukiyar talakawa ne ba su son a sake samun wani Buharin, Garba Shehu

A wani labarin daban, Fadar Shugaban Kasa ta ce manyan mutane masu aikata rashawa ne ba su son a sake samun 'wani Buhari' a Najeriya saboda wata manufarsu na gina kansu, Daily Trust ta ruwaito.

Mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce zai yi wahala a samu wani shugaba da zai iya zarce irin ayyukan da Buhari ya yi.

Kara karanta wannan

Babban Sarki a Najeriya ya shawarci Buhari ya dawo da shirin WAI, tare da zartar da hukuncin kisa ga 'yan ta'adda, matsafa da dillalan miyagun kwayoyi

Ya yi bayanin kan dalilin da yasa Buhari ba zai 'bari a cigaba da yadda ake harka' a kasar ba a karkashin gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel