Ziyarar Kaduna: El-Rufai ya kashe Naira miliyan 115 domin ba Buhari kariyar kwana 2

Ziyarar Kaduna: El-Rufai ya kashe Naira miliyan 115 domin ba Buhari kariyar kwana 2

  • Kananan hukumomin jihar Kaduna sun bada gudumuwar N150m wajen ba shugaban kasa tsaro
  • Gwamnatin Nasir El-Rufai ta zabi kananan hukumomi 11 su bada kudi domin bada karin kariya
  • A takardar, an bukaci kowane shugaban karamar hukuma ya kawo N10m, na Zaria ya bada N15m

Kaduna - Mutane su na ta surutu a kan zargin da ake yi na cewa gwamnatin jihar Kaduna ta karbi N150m da sunan ba shugaban kasa kariya da kawo ziyara.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Mai girma Muhammau Buhari ya kai ziyara zuwa Kaduna inda ya kaddamar da wasu ayyuka da Nasir El-Rufai ya yi.

Takardar da ke yawo ta nuna gwamna El-Rufai ya karbi kudi daga hannun kowace karamar hukuma saboda daukar nauyin tsaron tawagar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Atiku shekaru 4 kadai zai yi idan ya hau mulki, Shugaban kwamitin yakin zabensa

Legit.ng Hausa ta bibiyi lamarin inda ta fahimci kananan hukumomi 11 su ka hadu suka tara kudin.

Su wane kananan hukumomi aka zaba?

Jama’a, Kaura, Zangon-Kataf da Chikun aka zaba daga yankin Kudancin jihar, sai Kaduna ta Arewa, Kaduna ta Kudu, Giwa da Igabi a yankin tsakiyar jihar.

Takardar da mu ka samu ta nuna a yankin Kaduna ta Arewa, Zaria, Soba da Sabon Gari ne kananan hukumomin da aka karbi wadannan kudin a hannunsu.

Ziyarar Kaduna
Takardar neman kudin tsaro
Asali: UGC

Kwamishinan harkokin kananan hukumomi na jihar Kaduna, ya umarci kowace karamar hukuma ta kawo Naira miliyan 150 da za a kashe wajen hidimar.

Shugaban karamar hukumar birnin Zaria da kewaye ne kadai aka bukaci ya kawo Naira miliyan 15.

Takardar Kwamishina

Takardar ma’aikatar kananan hukumomin ta fito ne daga ofishin darektan bibiyan ayyuka, Iliyasu Hussaini, a madadin kwamishina a ranar 19 ga watan Junairu.

Kara karanta wannan

Kotu ta yankewa wasu masu walder 4 daurin shekaru 7 a kurkuku saboda satar N15m

“Ina mai ba ku umarnin kawo wadannan kudi da za a bukata wajen samar da karin tsaro da zirga-zirga na ziyarar da mai girma shugaban kasa zai kawo zuwa Kaduna domin kaddamar da wasu ayyuka.”
“Ana bukatar ku tabbatar da bin umarnin da aka bada kamar yadda aka yi kasafi, tare da bin dokokin batar da kudi.”

Gwamnati ta yi magana

Gidan talabijin na Arise TV ta tuntubi kwamishinan kananan hukumomi, Dr. Shehu Makarfi wanda ya bayyana cewa an bukaci wadannan miliyoyin kudi.

Dr. Shehu Makarfi ya ce an kashe kudin ne wajen zirga-zirga, tsaro da kuma watsa labarai.

Zaben 2023

A jiya aka ji cewa ‘yan majalisar dokoki na jihohin Arewa maso gabas sun yi wa Gwamna Yahaya Bello mubaya'a, sun bi sahun ‘yan majalisar Arewa maso tsakiya.

An kuma ji cewa ‘Yan majalisar sun bada shawarar APC ta tsaida ‘dan takarar shugaban kasa a 2023 daga Arewa saboda ‘Yan Kudu sun yi shekara 14 su na mulki.

Kara karanta wannan

Watanni bayan dakatar da ita, Hadiza Bala Usman ta ga shugaba Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel