Takarar Yahaya Bello ta samu kwarin-gwiwa, ‘Yan majalisan jihohin Arewa 6 na tare da shi

Takarar Yahaya Bello ta samu kwarin-gwiwa, ‘Yan majalisan jihohin Arewa 6 na tare da shi

  • ‘Yan majalisar dokoki na duka jihohin Arewa maso gabas sun ce su na goyon bayan Gwamna Yahaya Bello
  • Wadannan ‘yan majalisa za su marawa Yahaya Bello baya wajen zama ‘dan takarar APC a zaben 2023
  • Hon. Abubakar Sadiq Ibrahim shi ne shugaban ‘yan majalisan da ke goyon bayan Bello ya samu shugabanci

Bauchi - ‘Yan majalisan dokoki daga yankin Arewa maso gabashin Najeriya da ke karkashin jam’iyyar APC sun yi wa Gwamna Yahaya Bello mubaya’a.

Jaridar Leadership ta fitar da rahoto a yau Juma’a, 21 ga watan Junairu 2022 cewa ‘yan majalisar bangaren sun bi sahun takwarorinsu na Arewa maso tsakiya.

A wata sanarwa da ta fito daga bakin ‘yan majalisan jihohin, sun bayyana goyon bayansu ga neman takarar shugabancin kasan da Gwamnan Kogi yake yi.

Kara karanta wannan

Tseren shugabancin APC ya koma tsakanin Sanatoci 2, da tsohon Ministan Buhari

‘Yan majalisan jihohin Arewa maso gabashin kasar sun bada wannan sanarwa ne bayan wani taro da suka yi a wani otel mai suna Hazibal Suite a jihar Bauchi.

A ba Arewa tutan APC a 2023

A karshen zaman na su, ‘yan majalisar sun tabbatar da goyon-bayansu ga gwamnan na jihar Kogi, suka bada shawarar APC ta ba ‘dan Arewa tikitin takara a 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sun ce zuwa 2023 zai zama ‘yan Arewa sun yi mulkin shekaru 10, yayin da mutanen kudu sun yi shekara 14 su na mulki daga lokacin da aka dawo siyasa a 1999.

Yahaya Bello
Gwamna Yahaya Bello Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Jawabin bayan taro

"‘Yan majalisar dokoki da aka zaba daga jihohi shida na Arewa maso gabashin Najeriya sun yarda su goyi bayan ‘yanuwansu daga Arewa maso tsakiyar Najeriya su nemi takarar shugaban kasa a zaben 2023.”

Kara karanta wannan

Sani Bello: An fuskanci Farmaki 50, asarar rayuka 220 a Niger cikin watan Janairu

“Su ne yankin da aka hana samun shugabanci tun da Najeriya ta samu ‘yancin kai a 1960.”
“’Yan majalisar jihohinmu na Arewa maso gabas su na tabbatar da goyon bayansu ga matashin gwamna – Yahaya Bello, wanda yake neman zama shugaban kasa a 2023.”

- 'Yan majalisar

Wadanda suka sa hannu bayan taro su ne: Rt. Hon. Abubakar Sadiq Ibrahim, Hon. Bashir Mohammed, Hon. Nasir Abdulrahim, da Hon. Abubakar Shellong,

Aikin ku yana kyau

’Yan majalisar dokokin jihohin na Arewa maso gabas sun yaba da rawar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugaban APC, Mala Buni suke takawa.

A cewarsu, sun gamsu da kokarin shugaban kasa wajen hada-kan ‘yan Najeriya da yunkurin ganin ya gyara kasar nan kafin ya bar kan karagar mulki a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel