Abin da zai faru a 2023 idan aka yi sulhu tsakanin Ganduje da Kwankwasiyya inji Jagoran APC

Abin da zai faru a 2023 idan aka yi sulhu tsakanin Ganduje da Kwankwasiyya inji Jagoran APC

Jagoran APC, Injiniya Muaz Magaji ya yi magana game da makomar siyasar jihar Kano a zaben 2023

Muaz Magaji ya na ganin sulhu tsakanin Rabiu Kwankwaso da Abdullahi Ganduje zai lahanta su duka

Tsohon kwamishinan yace karshen Tsohon gwamnan jihar Kano da Ganduje ya zo idan aka sasanta

Kano - Injiniya Muaz Magaji ya na cikin wadanda suka je yi wa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ta’aziyyar rasuwar ‘danuwansa.

Injiniya Muaz Magaji wanda aka fi sani da Dansarauniya ya yi bayanin makomarsa siyasar Kano a lokacin da ake rade-radin dunkulewar manyan bangarori.

Jita-jita na yawo cewa akwai yiwuwar a sasanta tsakanin jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso da magajinsa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Tsohon kwamishinan ayyuka na Kano, Muaz Magaji yace idan har bangaren gwamna Abdullahi Ganduje ya sasanta da Rabiu Kwankwaso, karshensu ya zo.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun mamaye dajin Falgore, a kawo dauki: Ganduje ya kai kuka wajen Buhari

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake magana a shafinsa na Facebook, Dansarauniya yace sulhun ya na nufin wa’adin ritayar ‘yan siyasan na Kano ya zo idan suka ajiye bambancinsu.

Magaji da Rabiu Kwankwaso
Muaz Magaji da Rabiu Kwankwaso Hoto: @muaz.magaji
Asali: Facebook

Jagoran na tafiyar Win Win a Kano na cikin ‘yan tsagin G7 da suke rigima da bangaren gwamna Abdullahi Umar Ganduje a rikicin cikin gida na jam’iyyar APC.

Ta su ta zo karshe - Muaz Magaji, Dan Sarauniya

"Nayi imani, idan kaddara tasa a wannan gabar akai sulhu da HE (Mai girma gwamna Abdullahi Umar) Ganduje da HE Rabiu Musa Kwankwaso to wa'adin ritayarsu ce ta zo duk su biyun...
“Domin Allah ne mai zamani.”

- Injiniya Muaz Magaji

A cewar Injiniya Muaz Magaji, dalilinsa na fadan haka shi ne Allah mai zamani, a na shi ganin, karshen tsohon Gwamna Kwankwaso da Ganduje ta zo kusa.

Jim kadan bayan Magaji ya kai wa Sanata Kwankwaso ziyarar ta’aziyya na mutuwar Inuwa Kwankwaso, sai aka gan shi a gidan Malam Ibrahim Shekarau.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya bayar da auren diyar Sanata Shekarau a Kano

Da ya je gidan Sanatan Kano ta tsakiya, Shekarau, tsohon kwamishinan na Ganduje ya cire jar tagiyar da ya yafa a fadar Kwankwasiyya, ya rataya koren rawani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel