Shekaru bayan an manta an ci zabe, Jigon APC ya tona yadda aka tafka murdiya a zaben gwamna

Shekaru bayan an manta an ci zabe, Jigon APC ya tona yadda aka tafka murdiya a zaben gwamna

  • Tsohon mataimakin shugaban majalisar wakilai ya zargi APC da tafka murdiya a zaben jihar Osun
  • Da yake yankan fam din takarar gwamna, Hon. Lasun Yusuff ya fasa kwai, yace an yi magudi a 2018
  • Lasun Yusuff yace irinsu Omo-Agege aka yi da su domin a hana shi nasara a zaben fitar da gwani

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban majalisar wakilan tarayya, Hon. Lasun Yusuff, ya hakikance a kan murdiya aka yi a zaben gwamnan jihar Osun a 2018.

Jaridar This Day ta rahoto Honarabul Lasun Yusuff a makon da ya gabata, yana cewa an yi magudi a zaben gwamnan da aka kai ruwa rana ana yi a jihar Osun.

A cewar Lassun, Sanata Ovie Omo-Agege ya na cikin wadanda suke da hannu wajen wannan danyen aiki, don haka ne ma aka yi masa sakayya bayan zaben 2019.

Kara karanta wannan

Da addu'a zamu karbi mulkin Najeriya, matar Atiku ta magantu kan shirinsu a zaben 2023

‘Dan majalisar yace rawar da Omo-Agege ya taka, ta sa ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa.

“Bari a yau in tunawa ‘yan Najeriya cewa, ko zaben ‘yar tinke ce, ko kato-bayan-kato, rikicin ya fara ne a jihar Osun a 2018 da nufin ayi wa Lassun murdiya.”
“Mutane daga ko ina su ka rika kira na a kasar nan, su na cewa ka da in shiga zabe, su ka ce ko nawa zan kashe, asara zan yi domin magudi za ayi.” - Lassun.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lasun Yussuff
Hon. Lasun Yussuff Hoto: saharareporters.com
Asali: UGC

Daily Post ta rahoto Lassun ya na cewa Abdulaziz Yari ne wanda aka ba wannan aiki a zaben na gwamnan, amma ya gagara zuwa jihar Osun a lokacin zaben.

Ovie Omo-Agege ne ya yi aiki - Lassun

“Omo Agege ya zo kauyenmu, ya yi awa hudu a ranar zaben fitar da gwani, kuma ya shirya zabuka a mazabu uku a cikin shida da ke kauye na, ya sa hannu.”

Kara karanta wannan

EFCC ta cigaba da gabatar da hujjoji a kotu da za su sa a daure tsohon gwamna Fayose

Zuwa yanzu, Lassun bai iya kawo wata hujja da ke tabbatar da abin da ya fada ba. Tuni dai Ovie Omo-Agege ya yi watsi da wannan zargi da aka jefe shi da shi.

‘Dan siyasar ya yi wannan bayani ne a sakatariyar jam’iyyar APC yayin da ya je karbar fam na tsayawa takarar gwamna a zaben da za ayi a shekara mai zuwa.

Sai dai a zaben na 2022, Lassun Yusuf yace babu wanda ya isa ya sake yi masa abin da ya faru a baya. Lassun ya yi alkawarin ba zai yi amfani da ‘yan daba ba.

Yemi Osinbajo yace ka da a barke

Kwanaki aka ji Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo yace matsalolin da suka damu Najeriya irinsu talauci, za su ninku idan har aka raba kasar nan.

Yemi Osinbajo ya fadawa ‘yan kungiyar magoya-bayan muhimmancin hadin-kan Najeriya, tare da yi masu albishiri da cewa za a magance matsalar rashin tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel