Da Dumi-Dumi: A karon Farko Soludo ya sha kasa a wata karamar hukumar, Ubah ya lashe zabe

Da Dumi-Dumi: A karon Farko Soludo ya sha kasa a wata karamar hukumar, Ubah ya lashe zabe

  • Ɗan takarar gwamna karkashin jam'iyyar APGA ya sha ƙasa a karamar hukuma ɗaya, karon farko tun bayan fara sanar da sakamako
  • Sanata Ubah na jam'iyyar YPP, shine ya lashe karamar hukumar Nnewi ta Arewa, inda ya lallasa abokan takararsa
  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC na cigaba da aikin tattara sakamakon zaɓen gwamnan Anambra

Anambra - Ɗan takarar gwamna karkashin jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), Farfesa Chukwuma Soludo, ya sha ƙasa a ƙaramar hukuma ɗaya.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) na cigaba da aikin tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Anambra da aka gudanar jiya Asabar.

Dailytrust ta rahoto cewa Farfesa Soludo ya samu kuri'u mafi rinjaye a baki ɗaya kananan hukumomin da aka sanar da sakamakon su zuwa yanzun.

INEC na tattara sakamako
Da Dumi-Dumi: A karon Farko Soludo ya sha kasa a wata karamar hukumar, Ubah ya lashe zabe Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Sai dai kuma, Sanata Ifeanyi Ubah, ya lashe ƙaramar hukumar Nnewi ta Arewa, yankin da ya fito a jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Soludo ya lashe karamar hukumar Anaocha, mahaifar 'yan takara uku

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya sakamakon zaben ya kasance?

Ubah, wanda ɗan majalisa ne mai wakiltar mazaɓar Anambra ta kudu a majalisar dattijan Najeriya, shine ɗan takarar Young Progressives Party (YPP) a zaɓen gwamna.

Ubah da jam'iyyarsa ta YPP, ya samu kuri'u 6,485, yayin da farfesa Soludo na jam'iyyar APGA ya samu kuri'u 3,369 a karamar hukumar Nnewi ta Arewa.

An garkame ma'aikatan INEC

Wasu mutane sun nuna fushinsu kan ma'aikatan INEC bayan kammala zaɓe ana tattara sakamako a karamar hukumar Orumba ta Arewa

Rahoto ya bayyana cewa ma'aikatan ne suka nemi barin cibiyar tattara sakamakon gundumar Oko II domin su koma ofishin INEC.

Lamarin ya yi ƙamari sosai domin sai bayan sojoji sun shiga lamarin sannan komai ya saitu, inda suka kwashe kayan aikin zabe masu muhimmanci zuwa ofis.

A wani labarin kuma Rikicin cikin gida a APC ya tsananta yayin da gwamna Buni ya dakatar da kwamitin zaɓen shugabannin APC na wannan jihar.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra Jami’in INEC ya tsere da takardun sakamakon zabe sama da 40

APC ta kasa shawo rikicin dake faruwa a cikinta na Zamfara tun bayan sauya shekar gwamnan jihar, Bello Matawalle.

Ɓangaren tsohon gwamnan jihar, Abdul-Aziz Yari, da kuma tsohon Sanata, Kabir. Marafa, na ganin babu yadda za'ai a kwace jagorancin APC daga hannun su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel