Zaben Anambra Jami’in INEC ya tsere da takardun sakamakon zabe sama da 40

Zaben Anambra Jami’in INEC ya tsere da takardun sakamakon zabe sama da 40

  • Wani jami'in tattara sakamako ya tsere da takardun sakamakon zabe a wata karamar hukumar jihar Anambra
  • An ce ya samu damar guduwa da takardun sakamakon zabe sama da 40, kamar yadda INEC ta sanar
  • An dawo hutu bayan mintuna sama da 40, a halin yanzu za aci gaba da sanar da abubuwan da suka faru a rumfunan zabe

Anambra - Daily Trust ta ruwaito cewa, wani jami’in tattara sakamakon zaben gwamna da ke gudana a jihar Anambra ya tsere da takardun sakamakon zabe 42.

Dr. Gabriel Odor, jami’in tattarawa a karamar hukumar Idemili ta Kudu a Anambra, ne ya sanar da hakan a hedkwatar ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ke Awka, babban birnin jihar, yayin tattara sakamakon karshe a ranar Lahadi.

Da dumi-dumi: Jami’in INEC ya tsallake rijiya da baya da sakamakon zabe sama da 40
Wurin karbar sakamakon zaben jihar Anambra | Hoto: legit.ng
Asali: UGC

Odor, wanda malami ne a jami'ar Calabar, ya ce sace takardun sakamakon, ba a iya gudanar da zabe a yankunan da abin ya shafa ba, haka Leadership ma ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rahoto: INEC ta tabbatar da batun sace akwatin zabe a wasu rumfuna a zaben Anambra

Farfesa Chukwuma Soludo, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APGA), ya yi nasara a Idemili ta Kudu.

Ya samu kuri’u 2,312 inda ya doke Mista Valentine Ozigbo na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 2,016 da Sanata Andy Uba na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 1,039.

Ana ci gaba da tattarawa na karshe na sakamakon zaben gwamna na jihar Anambra.

Soludo ya lashe karamar hukumar Anaocha, mahaifar 'yan takara uku

A wani labarin, Jam’iyyar APGA ta lallasa jam'iyyar tsohon gwamnan jihar Anambra, Mista Peter Obi, da Sanata Uche Ekwunife, a karamar hukumarsu, This Day ta ruwaito.

Dukansu ‘yan karamar hukumar Anaocha ne, kuma ‘ya’yan jam’iyyar PDP ne. Shi ma dai Sanata Victor Umeh ya fito daga karamar hukumar.

Kara karanta wannan

Zuwa yanzu INEC ta karbi sakamakon zaben kananan hukumomi 19 cikin 21

Dokta Okene Isaac, malami a Jami’ar Calabar, wanda shi ne jami’in tattara bayanan kananan hukumomi ya ce: “Jimillar masu kada kuri’a 109860, sun amince da kada kuri'u 15940."

Asali: Legit.ng

Online view pixel