An dakatad da Likita da Malamar jinya da aka kama suna lalata cikin asibiti

An dakatad da Likita da Malamar jinya da aka kama suna lalata cikin asibiti

  • Likiti mai neman kwarewa a aiki da wata Malamar jinya na gab da fuskantar fushin hukumar asibiti
  • An dakatad da ma'aikatan biyu bayan zarginsu da kwanciya da juna a asibiti suna damun majinyata
  • Kwamishanan yankin ya ce an kafa kwamiti na musamman domin gudanar da bincike kan su

Tanzania - Majinyata sun kai karar wani Likita da Malamar jinya da suka saba yin lalata cikin asibiti, kuma hakan yayi sanadiyar dakatad da ma'aikatan biyu.

Mwananchi.co.tz ta ruwaito cewa wannan abu ya auku ne a wani asibiti dake Tabora, kasar Tanzania.

A cewar rahoton, Likitan wanda mai neman kwarewa ne da Matar sun saba shiga daya daga cikin dakunan asibitin suna shagalinsu kuma masu jinya na jinsu.

Da majinyatan suka gaji da jinsu kullum sai suka kai kararsu wajen shugabannin asibitin.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun kaure da cacar baki kan rashin adalci a daukar ma'aikata a rundunar soji

An dakatad da Likita da Malamar jinya da aka kama suna lalata cikin asibiti
An dakatad da Likita da Malamar jinya da aka kama suna lalata cikin asibiti
Asali: Depositphotos

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwamishanan yankin Kaliua, Paul Chacha ya yi ganawa ta musamman da ma'aikata ranar Litinin, 29 ga Nuwamba, inda ya sanar da dakatad da ma'aikatan.

Ya bayyana cewa an kafa kwamitin ladabtarwa domin gudanar da bincike kan lamarin kuma sakamakon binciken zai fadi matakin da za'a dauka kansu.

Ya tabbatarwa jama'a cewa ba za'a sassauta musu ba idan kwamitin bincike ta kamasu da laifi.

Tuko.co.ke. ta ruwaito Kwamishana Chacha da cewa:

"Idan wannan mutumin mai neman kwarewa ne, kamata yayi Asibitin ta rika lura da abubuwan da yake yi. Ta wani dalili za'a bar shi yayi haka?"

Asali: Legit.ng

Online view pixel