Betta Edu: Jerin Muhimman Abubuwa 10 da Ya Kamata Ku Sani Game da Ministar da Tinubu Ya Dakatar

Betta Edu: Jerin Muhimman Abubuwa 10 da Ya Kamata Ku Sani Game da Ministar da Tinubu Ya Dakatar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT Abuja - A ranar Litinin, 8 ga watan Janairu, 2024, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da Betta Edu, ministar harkokin jin ƙai da yaye talauci.

Ajuri Ngelale, kakakin Tinubu ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta wallafa a shafinta na manhajar X.

Ministar harkokin jin kai da aka dakatar, Betta Edu.
Edu: Jerin Muhimman Abubuwa 10 Ya Kamata Ku Sani Game da Ministar da Tinubu Ya Dakatar Hoto: Dr. Betta Edu
Asali: Twitter

Shugaban ƙasar ya ɗauki wannan matakin ne domin bada damar gudanar da cikakken bincike kan badaƙalar Naira miliyan N585m a ma'aikatar da take jagoranta.

Lamarin ya ƙara tada hazo ne bayan wata takarda ta bayyana mai ɗauke da sa hannun Betta Edo, kuma ta aika zuwa ofishin Akanta Janar na tarayya.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Jerin masu mukamin da Tinubu ya nada kuma ya dakatar/cire su kasa da shekara 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda takardar ta kunsa, ministar ta bada umarnin tura waɗannan kuɗaɗe zuwa asusun kai da kai na Oniyelu Bridget Mojisola.

Jerin abubuwan da ya kamata ku sani game da Edu

Legit Hausa ta tattaro maku wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da dakatacciyar ministar, ga su kamar haka:

1. An haifi Betta Edu a ranar 27 ga watan Oktoba, 1986.

2. Betta ta fito ne daga karamar hukumar Abi a jihar Kuros Riba da ke shiyyar Kudu maso Kudancin Najeriya.

3. Ta riƙe kujerar shugabar mata ta jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

4. Ta kasance kwamishinar lafiya ta jihar Kuros Riba har sai da ta yi murabus a shekarar 2022.

5. Ta kuma riƙe muƙamin shugabar kungiyar kwamishinonin lafiya ta Najeriya.

6. A shekarar 2015, Edu ta zama mafi karancin shekaru da aka nada a matsayin mai ba gwamnan jihar Kuros Riba, Benedict Ayade, shawara kan harkokin kiwon lafiyar al’umma a matakin farko.

Kara karanta wannan

Okupe: Tsohon hadimin shugaban ƙasa ya fice daga jam'iyyarsa, ya bayyana muhimmin dalili

7. A 2020, ta zama shugabar Kwamitin yaƙi da cutar COVID-19 ta jihar Kuros Riba.

8. An rantsar da Betta a matsayin ministar harkokin jin kai da kawar da fatara sannan kuma jam’iyyar APC ta maye gurbinta a matsayin shugabar mata ta kasa a 2023.

9. Haka nan a sa'o'i 48 da suka gabata, rahotanni kan zargin ministar harkokin jin ƙai, Betta Edu, da hannu a badaƙalar N585m suke cin kasuwa a soshiyal midiya.

10. An dakatar da ita daga matsayin ministar jin ƙai a ranar Litinin, 8 ga watan Janairu, 2024.

EFCC ta gayyaci Betta Edu

A wani rahoton kuma Dakatacciyar ministar jin ƙai da yaƙi da fatara, Betta Edu, ta samu gayyata daga hukumar yaƙi da cin hanci ta EFCC.

Gayyatar na zuwa ne bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da ita bisa zarge-zargen da ake mata na aikata ba daidai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel