Dan Kwankwaso da Tsofaffin Kwamishinoni Sun Kinkimo Rigima da Gwamnatin Abba
- PCACC ta dauki matakin kwato motocin gwamnati daga hannun tsofaffin kwamishinoni biyar da suka yi murabus daga gwamnatin Abba Kabir Yusuf
- Hukumar ta bayyana cewa ta kwato motocin ne bayan kwamishinonin sun yi biris da umarnin da aka ba su na su dawo da su
- Sai dai, tsofaffin kwamishinonin na Kano sun garzaya kotu domin kalubalantar matakin kwace motocin daga hannunsu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Takaddamar da ta biyo bayan kwato motocin da gwamnatin jihar Kano ta yi daga hannun tsofaffin kwamishinoni ta ɗauki sabon salo.
Tsofaffin kwamishinonin guda biyar sun shigar da gwamnatin jihar kara a gaban kotun ma'aikata ta kasa.

Source: Facebook
Takardun da jaridar Daily Trust ta samu sun nuna cewa AVM Umar, wanda ya yi aiki a matsayin kwamishinan tsaron cikin gida kafin yin murabus a watan Janairu, ya shigar da kara mai lamba NICN/KN/14/2026 kan babban lauyan jihar Kano da wasu mutane biyu.
An kwato motoci a hannun tsofaffin kwamishinoni
Hukumar karɓar korafe-korafe da Yaki da cin hanci da rashawa ta jihar (PCACC) ta ƙwato motocin ne a ranar Alhamis, 26 ga watan Fabrairun 2026 daga gidajen tsofaffin kwamishinonin.
Kwamishinoni biyar ɗin, waɗanda suka haɗa da Nasiru Sule Garo (Ayyuka na musamman), AVM Ibrahim Umar (Tsaron cikin gida), Adamu Aliyu Kibiya (Al’amuran jin ƙai).
Yusuf Ibrahim Kofar Mata (Kimiyya da fasaha), da kuma Mustapha Rabiu Kwankwaso (Matasa da wasanni), sun yi murabus ne jim kaɗan bayan ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
Me aka ce a cikin karar?
A cikin ƙarar, ya bayyana cewa jami’an PCACC sun kutsa cikin gidansa da ƙarfi a ranar 26 ga watan Fabrairu 2026, inda suka tsorata iyalinsa tare da ƙwace motarsa.
Mai shigar da ƙarar yana neman a gaggauta mayar masa da motar tare da bayyana mutanen da suka kai samamen.
An yi zargi kan gwamnatin Abba

Kara karanta wannan
Matakin da gwamnatin Kano ta dauka kan dan Kwankwaso da kwamishinonin da suka bar Abba
A wata sanarwar manema labarai daban da Umar ya sanya wa hannu a madadin tsofaffin kwamishinonin da abin ya shafa, sun zargi gwamnatin da nuna halin bita da kulli da kuma tsoratarwa, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Sun kafa hujja da cewa a ƙarƙashin dokar hukumar ƙasafi da rarraba kuɗaɗen shiga (RMAFC) ta shekarar 2023, motocin gwamnati suna daga cikin haƙƙoƙin da jami’an siyasa suka cancanci samu.

Source: Facebook
Sanarwar ta tuna cewa tsohon kwamishinan sufuri wanda ya yi murabus tun da wuri, Ibrahim Ali Namadi, an bar shi ya tafi da motarsa, don haka suka nace cewa su ma ya kamata su samu irin wannan gata.
Sun yi zargin cewa jami’an gwamnati ba motocin kawai suka ƙwace ba, har ma da motocin iyalansu na kashin kai suka kwashe yayin da su tsofaffin kwamishinonin ba sa gida.
Gwamnatin Abba ta musanta cin zarafin 'yan adawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf, ta yi martani kan zargin cin zarafin 'yan adawa.
Gwamnatin ta yi watsi da zarge-zargen da ke cewa tana kamawa, tsarewa, da cin zarafin mutanen da ke sukar Gwamna Abba.
Hakazalika, ta bayyana cewa tana nan kan bakanta wajen kare haƙƙoƙin ɗan adam, har da ’yancin faɗar albarkacin baki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
