Wata Sabuwa: Halin da El Rufai Ya Shiga yayin da Yake Tsare a Hannun ICPC
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC na ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai
- Mai ba El-Rufai shawara kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye, ya fito ya yi bayani kan halin da El-Rufai yake ciki a hannun hukumar
- Maganganunsa na zuwa ne yayin da tsohon gwamnan ya maka hukumar yaki da cin hancin kara a gaban wata babbar kotun tarayya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da cin hanci da ta rashawa ta ICPC ba ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ba.
Hukumar ICPC ta ki bayar da belin ne kwanaki takwas bayan tsare shi, lamarin da sam bai yi wa lauyoyinsa da iyalansa dadi ba.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba El-Rufai shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya fitar a ranar Litinin, 23 ga watan Fabrairun 2026 a shafinsa na X.
ICPC na ci gaba da tsare Nasir El-Rufai
Muyiwa Adekeye ya bayyana cewa tsohon gwamnan na Kaduna yana tsare tun bayan da ya kai kansa ofishin hukumar EFCC ranar 16 ga Fabrairu, 2026, domin amsa gayyatar da aka yi masa.
A cewar sanarwar, EFCC ta tsare El-Rufai ne har zuwa daren 18 ga Fabrairu, inda daga baya aka mika shi ga hannun hukumar ICPC.
'An ki ba da belin El-Rufai' - Hadiminsa
Adekeye ya ce lauyoyin El-Rufai sun miƙa takardar neman beli ga ICPC tun ranar 19 ga Fabrairu, amma har yanzu ba su samu amsa ba.
Ya ƙara da cewa, har yanzu ba a nuna wa tawagar lauyoyin takardar umarnin kotu da ke ba da damar ci gaba da tsare shi ba, duk da cewa wa’adin sa’o’i 48 da tsarin mulki ya amince da su na tsare mutum ba tare da tuhuma ba ya riga ya cika.
Adekeye ya bayyana cewa akalla akwai kararraki kotu guda biyu da suka shafi El-Rufai da aka tsara gudanarwa a wannan makon.
Za a saurari ƙarar da ya shigar na neman kare haƙƙin ɗan adam a gaban babbar kotun tarayya a ranar 25 ga watan Fabrairu, inda yake ƙalubalantar gwamnatin tarayya, ICPC, EFCC, da kuma DSS. Ƙarar na neman kotu ta ba da umarnin ba shi beli.
An kuma tsara za a gurfanar da shi a gaban kotu a ranar 25 ga watan Fabrairu kan wasu tuhume-tuhume da rahotanni suka ce hukumar DSS ce ta shigar da su.
Yadda ta kaya tsakanin El-Rufai, ICPC
Yayin da yake bayyana jerin abubuwan da suka faru, Adekeye ya ce jami’an ICPC sun binciki gidan El-Rufai da ke Aso Drive a ranar 19 ga Fabrairu 2026.

Source: Twitter
Lauyansa, Ubong Akpan, ya yi Allah-wadai da binciken, inda ya bayyana shi a matsayin haramtacce kuma wanda aka gudanar da shi da takardar bincike mara inganci.
Sakamakon haka, El-Rufai ya garzaya babbar kotun tarayya, inda yake neman kotun ta ayyana takardar binciken a matsayin maras inganci saboda rashin ƙwaƙƙwaran dalili da kuma kura-kurai na rubutu.
Waɗanda aka shigar da ƙarar a kansu sun haɗa da ICPC, babban majistare na Abuja, Sufeto janar na ’yan sanda, da kuma Ministan shari’a na kasa.

Kara karanta wannan
Bayan kanannaɗe El Rufai, ana zargin gwamnatin Tinubu ta shirya cafke tsohon gwamna
El-Rufai yana kuma neman kotun ta hana amfani da duk wani abu da aka kwashe a gidan nasa a matsayin shaida a kowace irin shari’a da za a yi da shi.
Sheikh Maraya ya yi zargi kan El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Halliru Maraya, ya jefi tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da wasu zarge-zarge.
Sheikh Halliru Maraya ya yi zargin cewa El-Rufai ya nuna bambanci wajen aiwatar da dokar hana daukar nauyin mahajjata da ya kafa a shekarar 2015.
Shehin darikar Tijjaniyar kuma tsohon mai ba da shawara a gwamnati ya nuna cewa yadda aka gudanar da tsarin ya sha bamban da yadda aka sanar da shi a farko.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

