Dalilin Buhari da Tinubu na Korar Janar 500 daga Rundunar Tsaro duk da Matsalar Ta'addanci
- Sama da Janar 500 ne aka tilasta musu ritaya daga rundunonin sojojiin Najeriya tun daga zamanin Muhammadu Buhari zuwa lokacin Bola Tinubu
- Wannan na da alaƙa da tsohuwar al’adar sojoji ta korar manyan hafsoshi da suka fi sababbin hafsoshin soja ƙwarewa ko suka yi horo ɗaya da su
- Wasu masana harkar tsaro sun bayyana cewa wannan tsari yana kawo cikas ga tsarin aiki, da kuma kara jefa sojoji cikin rudani
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Rahotanni sun nuna cewa daga shekarar 2015 zuwa 2023, an sallami fiye da Janarori 500 daga rundunar ƙasa, ruwa da na sama.
An yi wannan canji ne sakamakon canjin hafsoshin soja da aka yi a mulkin Muhammadu Buhari da Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan
Bayan Tinubu ya naɗa sababbin hafsoshin tsaro, an canjawa Janar sama da 60 wurin aiki

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa a lokacin da Buhari ya nada sababbin hafsoshi a 2015 — Buratai, Sadique Abubakar da Ibok-Ete Ibas, an tilasta ritayar Janar 100 da wasu hafsoshi 20 na rundunar ruwa.
An karo manyan jami'an sojan Najeriya
Haka kuma, a shekarar 2021 lokacin da tsohon Shugaba Buhari ya sake nadin sababbin shugabanni, sojoji fiye da 200 sun yi ritaya.

Source: Facebook
Mutuwar tsohon Shugaban rundunar sojan kasa, Ibrahim Attahiru a watan Mayu 2021 ta jawo karin ritaya ga Janar guda 20 da suka fi sabon hafsan sojojin ƙwarewa.
A lokacin Tinubu kuma, makonni biyu bayan ya hau mulki a Yuni 2023, ya nada Taoreed Abiodun Lagbaja, Hasan Abubakar da Emmanuel Ogalla a matsayin hafsoshin ƙasa, sama da ruwa.
Wannan ya jawo ritayar Janar 51, hafsoshin sama 49 da hafsoshin ruwa 17. Sababbin nade-naden da Tinubu ya yi kwanan nan suna iya jawo ritayar kusan hafsoshi 60.
Masana tsaro sun yi martani
Tsohon Janar Ishola Williams ya soki tsarin da gwamnati ke korar manyan hafsoshi, yana cewa hakan alama ce ta mulkin soja da ya kamata a daina.
Tsohon Janar Aliyu Momoh ya yaba wa Tinubu bisa sauye-sauyen da ya yi amma ya nemi a cire abin da ke hana rundunonin aiki yadda ya dace.
Wani tsohon hafsa, Sadique Shehu, ya bayyana cewa Najeriya tana da yawan Janarori fiye da kima — har kusan 960 a 2022 — wanda ya ce ya fi ƙarfin tsarin sojojin ƙasar.
Wasu masana sun nuna babu matsala a hakan domin tsohuwar al'ada ce ta gidan soja. Kamar yadda aka sani, babba shi yake ba karami umarni ya bi.
Idan aka nada sabon hafsun sojoji, dole wadanda ke gaban shi su ajiye aiki.
Haka zalika wasu masana na ganin ba za a iya aiki da Janar -Janar kusan 350 a lokaci guda ba don haka dole ne wasu jami'an su ajiye aiki domin a jawo wasu.

Kara karanta wannan
Sojoji sun kama karin mutane 26 da ake zargi da hannu a shirya yi wa Tinubu juyin mulki
A cikin wata tattaunawa da majiyar Legit, tsohon soja Abdullahi Bokaji Adamu ya bayyana cewa matakin korar sojojin baya-bayan nan na da nasaba da siyasa.
Ya ce:
“A gani na, korar hafsoshin tsaro kwanan nan na iya zama sakamakon abubuwa da dama. A hukumance, ana iya cewa gwamnati na son ganin an yi ingantaccen aiki da sababbin dabaru wajen magance matsalar tsaro da ta daɗe tana cin kasar nan."
“Amma a bayan fage, akwai yiwuwar siyasa ta shiga cikin al’amarin ko kuma akwai rikici na cikin gida a tsarin.”
Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda
A baya, mun wallafa cewa sojojin da ke aikin tsaro a jihar Kebbi sun samu nasarar kashe ‘yan bindiga fiye da 80 da suka yi yunkurin kutsawa jihar daga iyakar Zamfara.
Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba gwamna shawara kan harkokin sadarwa da tsare-tsare, Abdullahi Idris Zuru, ya fitar a ranar Lahadi, 26 ga Oktoba, 2025.
An yi wannan artabu ne a karamar hukumar Ngaski, bayan an tura dakarun zuwa yankunan da ke iyaka da jihohin Sokoto, Zamfara da Neja, kamar yadda Gwamna Nasir Idris ya umarta.
Asali: Legit.ng
