Digiri Dan Kwatano: Cikakken Jerin Jami'o'in Najeriya 9 Da Ake Bincikarsu a Yanzu

Digiri Dan Kwatano: Cikakken Jerin Jami'o'in Najeriya 9 Da Ake Bincikarsu a Yanzu

 • Biyo bayan rahoton jami'a wacce ta bada satifiket na bogi a Kwatano, Jamhuriyar Benin, gwamnatin Najeriya ta dauki matakin tsaftace bangaren ilimin manyan makarantu
 • Ma'aikatar Ilimi ta dakatar da amincewa da tantance digiri daga Jamhuriyar Benin da Togo, yayin da NUC ta fara aiki domin kawar da jami'o'in bogi a Najeriya
 • NUC ta jero wasu jami'o'i tara da za a bincika, ta gargadi wadannan jami'o'in cewa NYSC ba za ta amince da dalibansu ba, kuma ba za su iya neman aiki ba ko cigaba da karatu

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

A yayin da binciken karkashin kasa da wani dan jarida ya yi na tona asirin jami'a da ke bada satifiket din bogi a Kwatano, Jamhuriyar Benin, gwamnatin Najeriya ta dauki matakan tsaftace bangaren karatun manyan makarantu.

Kara karanta wannan

NUC ta fitar da cikakken jerin sunayen jami'o'in da aka haramta a Najeriya

A ranar Talata, 2 ga watan Janairu, Ma'aikatar Ilimi na Tarayya ta dakatar da karba tare da tantance satifiket daga Jamhuriyar Benin da Togo.

An fara bincikar jami'o'i tara a Najeriya bayan rahoton digiri dan Kwatano
NUC ta fara bincikar jami'o'i 9 a Najeriya. A LURA: Mutanen da ke hoton nan basu da alaka da labarin, an yi amfani da su ne kawai don misali. Hoto: recep-bg, visual vic
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar Kula da Jami'o'i na Kasa (NUC) ta jadada cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba sai ta kawar da jami'o'in bogi a kasar.

Chris Maiyaki, mukadashin sakataren NUC, a baya-bayan nan ya ce hukumar ta kama wasu mutane da suka kafa jami'o'i ba bisa ka'ida ba a Najeriya.

NUC ta lissafa jami'o'i 9 da ake bincika a yanzu

Sai dai, a wallafar ta na baya-bayan nan, NUC ta saki jerin jami'o'i 58 wadanda aka kafa ba bisa ka'ida ba a Najeriya da kuma wadanda a yanzu ake bincikarsu.

Jami'o'in da ake bincike kansu suna:

 1. National University of Nigeria, Keffi, Nasarawa state
 2. North Central University, Otukpo, Benue state
 3. Christ Alive Christian Seminary and University, Enugu
 4. Richmond Open University, Arochukwu, Abia state
 5. West Coast University, Umuahia
 6. Saint Clements University, Iyin Ekiti, Ekiti state
 7. Volta University College, Aba, Abia state
 8. Illegal Satellite Campuses of Ambrose Alli University
 9. L. I.F.E Leadership University, Benin City, Edo state

Kara karanta wannan

Digirin bogi: Ina cikin damuwa game da tsarona, in ji dan jaridar da ya saki rahoton 'digiri dan Kwatano'

A cewar NUC, duk wanda ya samu satifiket daga cikin jami'o'in da aka lissafa ya kuka da kansa.

"NYSC ba za ta karbi satifiket daga wadannan jami'o'in ba domin zuwa bautan kasa, ko samun aiki ko cigaba da karatu. An sanar da hukumomin tsaro da abin ya rataya a kansu su dauki mataki na gaba da ya dace," a cewar hukumar."

Benin: Shugaban Kungiyar Daliban Najeriya Ya Nemi a Kama Dan Jaridan da Ya Saki Rahoton ‘Digiri Dan Kwatano’

A wani rahoton, Shugaban Kungiyar daliban Najeriya da ke karatu a jamhuriyar Benin, Ugochukwu Favour ya nemi a kama Umar Audu, dan jaridar da ya fallasa rashin ingancin takardar digiri a jami'ar kasar.

Da ya ke hira da Channels TV a ranar Alhamis, Favour soki dan jaridar kan yadda ya bi wata barauniyar hanya ya sami takardar digiri a Benin ba tare da zuwa makarantar ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu za ta kara dakatar da karbar digiri daga wasu kasashe bayan Benin da Togo

Asali: Legit.ng

Online view pixel