Bayan Keffi, An Gano yadda Fursunoni Suka Tsere daga Gidajen Yari 10 a Shekara 5

Bayan Keffi, An Gano yadda Fursunoni Suka Tsere daga Gidajen Yari 10 a Shekara 5

  • Fursunoni 16 ne suka arce daga gidan yarin Keffi da ke jihar Nasarawa a ranar Litinin bayan da suka jikkata akalla jami’an tsaro biyar
  • Majalisar wakilai ta taba aika wa Shugaba Bola Tinubu bukatar kafa kwamitin bincike kan tserewar fursunoni 7,000 a cikin shekaru bakwai
  • A shekaru biyar, an farmaki gidan yarin Kuje da wasu 10, inda a wannan rahoto muka tattaro yadda fursunoni suka tsere daga gidajen yarin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Nasarawa - Tarihin fashin magarkama a Najeriya ya ci gaba a ranar Litinin bayan da fursunoni 16 suka tsere daga gidan yarin Keffi, jihar Nasarawa.

Legit Hausa ta ruwaito cewa fursunonin sun jikkata gandirebobi biyar a lokacin tserewarsu, amma hukumar NCoS ta ce an kamo bakwai daga cikinsu.

An samu fashe fashen gidajen yari 10 a Najeriya a tsakanin shekarar 2020 zuwa 2025.
Gidan gyaran hari na Suleja da ke jihar Neja da 'yan bindiga suka fasa. Hoto: Origo
Source: UGC

Kudurin majalisa kan tserewar fursunoni

Kara karanta wannan

Ana batun sulhu, yaran Bello Turji sun harbe mutane a Sokoto, sun sace mutum 16

A shekarar 2024, Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa majalisar wakilai ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa kwamitin binciken shari’a kan hare-haren gidajen yari a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin abubuwan da majalisar ke so Tinubu ya shi shi ne tabbatar da cewa irin wadannan hare-hare a kan cibiyoyin tsaron kasa ba su sake faruwa ba.

'Dan majalisa, Kabiru Alhassan Usman Rurum daga jihar Kano, cikin wani kudiri, ya koka kan yawan hare-haren da ake kai wa gidajen gyara hali da kuma yawan tserewar fursunoni.

A lokacin, dan majalisar ya bayyana cewa sama da fursunoni 7,000 sun tsere a fashe-fashen gidajen yari 17 a Najeriya daga Satumbar 2015 zuwa Yulin 2023.

Fashin gidajen yari 10 a shekara 5

Baya ga wannan sabon fashin magarkamar na Keffi, Legit Hausa ta binciko yadda fursunoni suka tsere daga gidajen yari 10 a cikin shekaru 5 kacal.

1. Koton Karfe

A watan Maris din 2025, fursunoni bakwai zuwa 12 a gidan yarin Koton Karfe da ke jihar Kogi, suka yi galaba a kan jami’an tsaro, suka kashe daya, suka daure biyu, sannan suka tsere.

Kara karanta wannan

Fursunoni sun farmaki jami'an NCoS, sun tsere daga gidan yarin Keffi

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa fursunonin sun fice daga gidan yarin ta wata kafar taga da ta rushe kafin a kawo dauki.

2. Suleja

Fiye da fursunoni 100 suka tsere daga gidajen yarin Suleja a jihar Neja, bayan ruwan sama mai tsanani ya lalata wani bangare na katangar gidan yarin a Afrilun 2024.

Legit Hausa ta ruwaito cewa jimillar wadanda suka tsere sun kai 118, amma hukumar NCos ta ce an yi nasarar kama 10 daga cikinsu.

3. Kuje

A ranar 5 ga Yuli, 2022, fursunoni 879 suka tsere daga gidan yarin Kuje da ke Abuja, a wani hari da kungiyoyin ISWAP da Ansaru suka kai, inda suka kubutar da manyan masu laifi.

Maharan dai sun yi ta harbi kan mai uwa da wabi sannan sun yi amfani da bama-bamai wajen samun iko kan hanyoyin shiga da fita daga cibiyar guda hudu.

4. Mandala

A ranar 2 ga Janairu, 2022, fursunoni uku suka tsere daga gidan yarin Mandala da ke Ilorin, jihar Kwara.

Daga cikinsu akwai mai jiran hukuncin kisa kan laifin fashi da makami da wasu biyu masu irin wannan tuhuma.

Kara karanta wannan

An kashe kusan N50trn: Manyan ayyuka 16 da Tinubu ya yi bayan cire tallafin mai

5. Kogi

A ranar 13 ga Satumba, 2021, aka kashe jami’an tsaro biyu yayin da aka kai hari gidan yarin Kabba, da ke jihar Kogi inda ‘yan bindigar suka saki fursunoni 240 daga cikin 294 da ake tsare da su.

Mun ruwaito cewa, an sake kama wasu daga cikin fursunonin da suka tsare a kusa da otal din Kudon, Kabba, lokacin da suka yi kokarin shiga abin hawa don guduwa zuwa jihar Kwara.

6. Filato

A ranar 8 ga Yuli, 2021, mutum hudu masu jiran shari’a kan satar mutane da fashi da makami suka tsere daga gidan yarin Jos, lamarin da aka dora alhakinsa kan sakacin jami’an tsaro.

7. Imo

A ranar 5 ga Afrilu, 2021, ‘yan bindiga suka kai hari a gidan yari na Owerri da ke cikin babban birnin jihar Imo tare da kubutar da fursunoni sama da 1500.

Maharan sun kuma kone hedikwatar rundunar 'yan sanda ta jihar Imo da ke Owerri tare da kona kusan dukkanin motocin da ke ajiye a helkwatar rundunar.

Kara karanta wannan

2027: 'Dan majalisa ya yi hasashe kan yiwuwar takara tsakanin Tinubu da Jonathan

Daruruwan fursunoni ne suka tsere daga gidajen yarin Najeriya 10 a cikin shekaru 5
Shugabannin hukumar gidajen yarin Najeriya yayin da suke duba gidan yarin Kuje. Hoto: @CorrectionsNg
Source: Twitter

8/9. Gidajen yari 2 a Benin

A ranar 19 ga Oktoba, 2020, fursunoni 1,993 suka tsere daga gidajen yari na Benin da Oko, Jihar Edo, bayan ‘yan daba sun kai hari a lokacin zanga-zangar #EndSARS.

Mun ruwaito cewa hukumar NCoS ta bayyana cewa:

''Mafi yawan fursunonin da suka tsere an riga an yanke masu hukuncin kisa, suna jiran mutuwa ne. Lallai sakin masu laifin barazana ne ga tsaron al'umma."

10. Ondo

A ranar Alhamis, 22 ga watan Oktoba ne masu zanga-zangar #EndSARS suka kai farmaki gidan yari da ke Okitipupa, hedkwatar karamar hukumar Okiyipupa da ke jihar Ondo.

A cewar rahoton Legit Hausa, akalla fursunoni 58 suka gudu daga gidan gyara halin kuma suka bankawa gidan yarin wuta dake.

An dakatar da manyan jami'an NCoS

A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya ta dakatar da wasu jami'anta bisa zarginsu da rashawa.

Kara karanta wannan

Jami'an 'yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga a Katsina, an ceto mutane

Hukumar ta sanar da cewa ta dauki matakin dakatar da jami'an ne domin ba ta damar gudanar da sahihin bincike kan zarge-zargen da ake yi masu.

Jami'an da aka dakatar sun hada da; Michael Anugwa (DCC) mai kula da matsakaiciyar cibiyar tsaro da ke a Kirikiri, Legas da Sikiru Adekunle (DCC) da ke kula da babbar cibiyar tsaro (MSCC) a Kirikiri, Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com