Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan yari, sun saki fursunoni 240 sannan suka kashe sojoji a Kogi

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan yari, sun saki fursunoni 240 sannan suka kashe sojoji a Kogi

  • ‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan gyara hali da ke Kabba, Jihar Kogi a daren ranar Lahadi, 12 ga watan Satumba
  • Sun saki akalla fursunoni 240 sannan suka kashe sojoji biyu tare da jikkata wani
  • Kakakin ma’aikatar gidan yari (NCoS), Mista Francis Enobore ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin

Kogi - Akalla fursunoni 240 ne suka tsere daga Cibiyar Tsaro ta MSCC da ke Kabba, Jihar Kogi, bayan wani hari da ‘yan bindigar da ba a san ko su wanene ba suka kai, Channels TV ta ruwaito.

Mai magana da yawun ma’aikatar gidan yari (NCoS), Mista Francis Enobore ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa harin ya faru ne da tsakar daren ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka fasto a Kaduna, El-Rufai ya yi martani mai zafi

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan yari, sun saki fursunoni 240 sannan suka kashe sojoji a Kogi
‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan yari, sun saki fursunoni 240 sannan suka kashe sojoji a Kogi Hoto: The Nation

A cewarsa, maharan da yawansu sun isa gidan gyara halin dauke da muggan makamai kuma nan da nan suka fafata da masu gadin gidan ta hanyar musayar wuta.

Mista Enobore ya ci gaba da bayyana cewa Kwanturola -Janar, Haliru Nababa ya ba da umurnin a fara aikin kamo su nan take tare da gudanar da cikakken bincike yayin da ya jagoranci wata tawaga don tantance halin da ake ciki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nababa ya kuma yi kira ga jama'a da su bai wa jami'an tsaro bayanan sirri masu amfani da za su taimaka wajen kamo wadanda suka tsere.

Jaridar The Nation ta kuma ruwaito cewa an kashe sojoji biyu da ke kan shingen bincike a gaban gidan gyara halin sannan kuma aka jikkata wani a lokacin da maharan suka kai farmaki.

Wata majiya ta tabbatar da cewa daga baya an sake kama wasu daga cikin fursunonin da suka tsare da misalin karfe 8 na safe ranar Litinin a kusa da Otal din Kudon, Kabba, lokacin da suka yi kokarin shiga abin hawa don tserewa zuwa jihar Kwara da ke makwabbtaka.

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

'Yan daba sun kai wa 'yan kwana-kwana hari a Kogi, sun raunata wasu sun lalata motar kashe gobara

A wani labari na daban, wasu ‘yan daba sun kai wa jami’in hukumar kashe gobara farmaki a Lokoja, jihar Kogi, inda suka yi musu kaca-kaca da makamai.

Jami’in hulda da jama’an hukumar, Ugo Huan, ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Juma’a wacce ya gabatar wa da manema labarai.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, takardar ta bayyana cewa lamarin ya auku ne a ranar Laraba akan titin Felele lokacin da jami’an hukumar kwana-kwanan suka nufi inda gobara ta kama wata mota a gidan man Al-Salam dake kallon Kogi State Polytechnic.

Asali: Legit.ng

Online view pixel