Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun fasa gidan yari da hedkwatar 'yan sanda, fursunoni sun tsere

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun fasa gidan yari da hedkwatar 'yan sanda, fursunoni sun tsere

- Wasu 'yan bindiga sun afkawa wani gidan yari da hedikwatar 'yan sanda a jihar Imo

- An bayyana cewa, sun kubutar da fursunoni tare da kone motocin 'yan sanda da dama

- Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar faruwar lamarin tare da shaida bincike akai

Wasu ‘yan bindiga a safiyar ranar Litinin sun kai hari a gidan yari na Owerri da ke cikin babban birnin jihar Imo tare da kubutar da fursunoni sama da 1500.

Maharan sun kuma kone hedikwatar rundunar 'yan sanda ta jihar Imo da ke Owerri tare da kona kusan dukkanin motocin da ke ajiye a helkwatar rundunar.

'Yan bindigar sun ci gaba da sakin wadanda ake zargin a kusan dukkanin magarkamu a sashin binciken manyan laifuka na rundunar.

KU KARANTA: Obasanjo ya bi sahun Gumi, ya roki gwamnatin Buhari ta yafewa tubabbun 'yan bindiga

Da duminsa: 'Yan bindiga sun fasa gidan yari da hedkwatar 'yan sanda a Imo
Da duminsa: 'Yan bindiga sun fasa gidan yari da hedkwatar 'yan sanda a Imo Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta tattaro cewa 'yan bindigan sun fara barnar ne daga karfe 1 na dare zuwa 3 na safiyar Litinin.

Sun rera wakokin hadin kai a gidan gwamnati da ke kusa na tsawon mintuna 30 kafin su far wa cibiyoyin, in ji majiyar tsaron ga wakilin Punch.

Yayin da suka kutsa kai cikin gidan yarin tare da taimakon ababen fashewa, maharan sun ce wa fursunonin da aka tsare da su koma gidajensu.

Lokacin da aka tuntube shi, kakakin ‘yan sanda a jihar, Orlando Ikeokwu, ya tabbatar da faruwar harin.

Amma, ya tabbatar wa mutanen jihar cewa hukumomin tsaro suna bincike kan lamarin.

KU KARANTA: Sakon Osinbajo ga 'yan Najeriya: Ku kara hakuri, abubuwa za su daidaita

A wani labarin, Rahotanni daga jihar Imo sun bayyana cewa mutum uku sun hallaka bayan wani hari da ake zargin Kungiyar mayakan Biafra ta kai wa al'ummar Hausawa da ke yankin Orlu a jihar ta Imo.

Lamarin dai ya jefa al'ummar Hausawan da ke yankin cikin zaman zulumi.

A cewar wani dan kasuwa Bahaushe mazaunin yankin na Orlu, Alhaji Amadu Ali, tun daga watan Agustan bara zuwa yanzu, kungiyar ta Biafra ta halaka Hausawa 12 baya ga asarar dukiya da suka tafka da haura ta kusan naira miliyan 42.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.