Bello Turji Ya Yi Sabon Bidiyo, Ya Tura Sako ga Pantami, Dan Bello da Malamin Musulunci

Bello Turji Ya Yi Sabon Bidiyo, Ya Tura Sako ga Pantami, Dan Bello da Malamin Musulunci

  • Dan ta'adda, Bello Turji ya sake fitar da bidiyo kan fitaccen lauya, Bulama Bukarti bayan fitar da wani rahoto
  • Bello Turji ya soki Bukarti inda ya ce rahoton da ya fitar akwai son rai a ciki ya kamata ya ji ta kowane bangare
  • Dan ta'addan ya kuma bukaci Sheikh Murtala Bello Asada ya shigo daji su hadu kan irin maganganu da ya ke yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Rikakken dan ta'adda, Bello Turji ya sake fitar da wani sabon bidiyo inda ya ke yin gargadi.

Bello Turji ya gargadi fitaccen lauya da ake kira Bulama Bukarti kan fitar da wasu takardu da ya yi game da haraji a garin Moriki.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace Bello Yabo? Shehi ya yi maganar 'garkuwa' da shi da 'kamen' DSS

Bello Turji ya yi sabon bidiyo kan Bello Asada da Isa Pantami
Dan ta'adda, Bello Turji ya sake fitar da sabon bidiyo. Hoto: Professor Isa Pantami, Sheikh Murtala Bello Asada.
Asali: Facebook

Asada: Bello Turji ya yi gargadi a bidiyo

Dan ta'addan ya fadi haka ne a wani bidiyo da @AM_saleeeem ya wallafa a shafinsa na X a yau Laraba 11 ga watan Satumbar 2024.

A cikin faifan bidiyon, Turji ya ce Bukarti ya wallafa gaskiya ne amma ya yi kuskure wurin fitar da bayanin.

Ya ce akwai kuskure a bayanan Bukarti inda ya ce ƙaryata maganar cewa ya kakaba haraji domin an kira masa shanu 50.

Har ila yau, Turji ya bukaci Bukarti da sauran karnukan Yahudawa har da Dan Bello da su ji ta bakin yan uwansa kafin yanke hukunci inda ya ce N50m ya kakabawa yan Moriki.

"Saboda yan Moriki ke da jini su wadanga ba su da galihu, to ku ji mutanen Moriki a nan kasa aka haife ni."

Kara karanta wannan

Fitaccen mawaki Musulmi ya zabgawa malamin addini mari a bidiyo, ya fadi dalili

"Shanun da aka kashe babu gonar wanda suka shiga, da ranar Allah a watan biyar aka hallaka su kan tudu ba wai gidan wani suka shiga ba."

- Bello Turji

Rokon Bello Turji ga Janar Christopher Musa

Bello Turji ya kuma roki Christopher Musa mai gidansu a cewarsa da ya yi wa Allah ya ba Sheikh Murtala Bello Asada mukami.

Ya ce idan ba zai ba shi mukamin soja ba ko shugaban 'yan banga ya ba shi saboda ya shiga daji.

Daga bisani, ya soki tsohon Minista, Farfesa Isa Pantami da ya ke zargin masu karbar muƙamin gwamnati inda ya ce da aka ba shi mukamin an neme shi an rasa.

Ta'addanci: Murtala Bello Asada ya zargi Matawalle

Kun ji cewa malamin Musulunci, Sheikh Murtala Bello Asada ya zargin karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle da hannu a ta'addanci.

Malamin ya ce tabbas Matawalle ya siyasa rikakkun yan ta'adda motoci ciki har da Bello Turji da kuma Ado Aliero.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.