An Shiga Alhini Bayan Sanar da Rasuwar Basarake Mai Daraja Ta 1 a Asibitin Kano

An Shiga Alhini Bayan Sanar da Rasuwar Basarake Mai Daraja Ta 1 a Asibitin Kano

  • An shiga jimami bayan sanar da rasuwar Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya a yau Lahadi
  • Marigayin mai shekaru 88 ya rasu da safiyar yau Lahadi a wani asibiti da ke jihar Kano bayan fama da jinya
  • Masarautar Ningi ta tabbatar da rasuwar marigayin inda ta ce za a yi sallar jana'iza da yammacin yau a fadar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bauchi - Allah ya karbi rayuwar Sarkin Ningi a jihar Bauchi, Mai Martaba, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya.

Marigayin ya rasu ne da safiyar yau Lahadi 25 ga watan Agustan 2024 a wani asibiti da ke Kano.

Sarkin Ningi ya riga mu gidan gaskiya a Kano
An sanar da rasuwar Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya. Hoto: Ibrahim Malam Goje.
Asali: Facebook

Bauchi: An sanar da rasuwar Sarkin Ningi

Kara karanta wannan

Kama jiragen Najeriya: An bukaci DSS ta yi gaggawar kama tsohon gwamnan APC

Sakataren masarautar Ningi, Alhaji Usman Sule shi ya tabbatar da rasuwar marigayin bayan ya sha fama da jinya, cewar RFI Hausa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce za a yi jana'izar marigayin mai shekaru 80 da misalin karfe 4.00 na yamma a fadarsa da ke Ningi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa basaraken ya rasu bayan shafe akalla shekaru 46 a kan karagar mulkin Ningi, Tribune ta tattaro.

Marigayin ya dare sarautar Ningi a shekarar 1978 inda ya yi sarauta har zuwa yau Lahadi 25 ga watan Agustan 2024.

Martanin dan marigayin kan rasuwar Sarkin Ningi

Dan marigayin, Alhaji Aminu Yunusa Danyaya ya tabbatar da mutuwar mahaifin nasu a yau Lahadi.

Aminu ya ce ya shirya tafiya Kano wurin mahaifin nasu inda aka sanar da shi cewa ya dakata saboda ya riga ya rasu.

Ya ce daman marigayin ya dade yana jinya inda ya ce a ranar Alhamis din nan da ta gabata ya dawo daga Saudiyya domin ganin likita.

Kara karanta wannan

Sarkin Gobir: Miyetti Allah ta yi magana kan kisan basaraken, ta fadi matsayarta

Masarautar Bauchi ya tube sanata daga sarauta

Kun ji cewa Masarautar Bauchi ta tuɓe rawanin sarautar gargajiya na ‘Majidadin Bauchi’ daga kan Sanata Shehu Buba Umar.

Masarautar ta ɗauki wannan matakin ne bisa zargin sanatan da rashin mutuntawa da cin mutuncin gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed.

Sanata Shehu Umar na wakiltar mazabar Bauchi ta kudu ne a Majalisar Dattawa ta 10 a karkashin jam’iyyar adawa a jihar watau APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.