Kotun Ɗaukaka Kara Ta Yanke Hukuncin Dauri a Shari'ar Sarkin da Aka Tsige Daga Sarauta

Kotun Ɗaukaka Kara Ta Yanke Hukuncin Dauri a Shari'ar Sarkin da Aka Tsige Daga Sarauta

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin da aka yankewa tsohon Baale na Shangisha Mutiu Ogundare kan laifin garkuwa da kansa
  • Alkalan kotun mai zama a Legas sun amince da hukuncin babbar kotun jiha amma sun rage masa zaman gidan kaso zuwa shekaru 12
  • Gwamnatin jihar Legas ta gurfanar da basaraken wanda aka tuɓe bisa tuhume-tuhume uku da suka shafi yin garkuwa ta ƙarya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Kotun daukaka kara da ke zamanta a jihar Legas ta tabbatar da hukuncin da aka yankewa sarkin Shangisha a Magodo da aka tuɓewa rawani, Mutiu Ogundare.

Kotun ta amince da hukuncin da ƙarama kotu ta yankewa basaraken bayan kama shi da laifin yin garkuwa da kansa domin neman kudin fansa.

Kara karanta wannan

Gwamna Dikko Radda ya kafa tarihi, ya ƙirkiro doka kan mata masu iddah a Katsina

Harabar kotu.
Kotun ɗaukaka kara ta amince da hukuncin ɗaurin shekaru 12 kan basarake a Legaa Hoto: Court of Appeal
Asali: Facebook

Channels tv ta tattaro cewa a watan Satumba, 2022, babbar kotun jihar Legas mai zama a Ikeja ta kama Ogundare da laifi kuma ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 15.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakamakon rashin gamsuwa da hukuncin, Ogundare ya garzaya kotun daukaka kara domin kalubalantar hukuncin da karamar kotun ta yanke.

Kotun ɗaukaka kara ta yi rangwame

Mai shari’a Paul Bassi wanda ya yanke hukuncin a madadin kwamitin alƙalai uku na kotun ɗaukaka ƙara, ya amince da hukuncin da karamar kotun ta yanke.

Mai shari’a Bassi ya ce karar da Ogundare ya ɗaukaka ta samu nasara a wani bangare wanda sakamakon haka aka rage masa zaman gidan yari zuwa shekaru 12.

Kotun ta ce basaraken da aka tuɓe daga mulki zai yi zaman gidan yari na shekaru 10 a laifi na farko da shekaru biyu kan laifi na biyu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai ƙazamin hari, sun kashe basarake mai martaba da ɗansa a Arewa

Dangane da laifi na uku kuma kotun ɗaukaka ƙara ta soke hukuncin babbar kotun jihar Legas.

Wasu laifuffuka basaraken ya aikata?

Tun farko kotun majistare ta Ogba ta garkame wanda ake tuhuma, Ogundare a a gidan yarin Kirikiri, bisa zarginsa da laifin yin garkuwa da kansa a watan Yuli, 2017.

An gurfanar da shi ne tare da matarsa, Abolanle, da dan uwansa, Opeyemi Mohammed, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Gwamnatin Legas ta gurfanar da su a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume uku da suka hada da hada baki, rashin zaman lafiya, da yin garkuwar ƙarya.

Kano: Ƴan daba sun farmaki ɗan majalisa

A wani rahoton kuma yan daba sun farmaki ɗan majalisar dokokin Kano a wurin taron saukar Alkur'ani wanda Aminu Ado Bayero ya halarta.

Hon Abdul-Majid Umar (NNPP) ya yi zargin cewa ƴan daban suna cikin tawagar sarki na 15 da aka tuɓe, zargin da hadimin basaraken ya musanta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262