Tsohuwar Shugaban kasan Malawi zata shigo Najeriya

Tsohuwar Shugaban kasan Malawi zata shigo Najeriya

– Tsohuwar Shugaban kasan Malawi ,Dakta. Joyce Banda ,zata shigo jihar Legas a wannan makon.

–Dakta Banda zata kasance mai magana a taron mata na Women’s Power Lunch

–Kungiyar Murtala Muhammed Foundation (MMF) ta shirya taron.

Tsohuwar shugaban kasan Malawi, Dr. Joyce Hilda Banda, ce zata zama babban bako mai magana a taron mata na Women’s Power Lunch. Dr. Banda , wata kayatatar yar kasuwa, yar yaki,yar siyasa , ita ce wacce ta assasa jam'iyyar People's Party a Malawi kuma itace shugaban kasa mace ta farko a kasar,na biyu a nahiyar Afrika.

Tsohuwar Shugaban kasan Malawi zata shigo Najeriya
Fmr Malawi President, Joyce Banda

A shekara 2013, Dr. Banda na daga cikin mutane 100 masu fada a ji a duniya game da mujallar Time Magazine A watan Disambar 2014, mujallar Forbes sun lakaba mata mace mafi karfi a nahiyar Afrika kuma ta 40 a duniya gaba daya. A shekarar 2014, tashar yada labarai ta CNN mace mafi fada aji a siyasa a duniya gaba daya..

Game da cewar Mrs Muhammad Oyebode, tace taron na gayyatar shugabanni mata daga sassan duniya gaba daya.

Ta ce : “Anyi abubuwa da yawa wajen tabbatar da cewan a samu daidaito tsakanin jinsi da kuma hakkin mata da yara a afrika. Amma akwai aiki a gaba, wadda ke bukatan mata su hada kai daga sassan duniyan nan domin zurfafa hadin kai da kirkiro sabbin hanyoyi na hadaka domin cimma manufar mu na yaki da banbancin jinsi da kuma kiyayyan mata a nahiyar afrika . wannan shine daya daga cikin manufofin wannan cibiya.

KU KARANTA : A rika sara ana duban bakin gatari –Sanata Ali Ndume

Karo na farkon taron ya gabatar da tsohuwar uwargidan shugaban kasa afrika ta kudu, Graca machel Mandela DBE, a matsayin mai magana.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng