Jirgin Sama Ya Yi Ɓatan Dabo Ɗauke da Mataimakin Shugaban Ƙasar Malawi da Mutum 9

Jirgin Sama Ya Yi Ɓatan Dabo Ɗauke da Mataimakin Shugaban Ƙasar Malawi da Mutum 9

  • Rahotanni na nuni da cewa jirgin da ke dauke da mataimakin shugaban kasar Malawi, Saulos Klaus Chilima ya bace
  • Wata sanarwa da ofishin shugaban kasa da ministocin Malawi ya fitar ta ce duk wani kokari na tuntubar jirgin ya ci tura
  • An ce jirgin ya tashi daga Lilongwe, babban birnin kasar da misalin karfe 9:00 na safiya amma har yanzu ba a ganshi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Wani jirgin sama dauke da mataimakin shugaban kasar Malawi, Saulos Klaus Chilima da wasu mutane tara ya bace, kamar yadda fadar shugaban kasar ta sanar a yau Litinin.

Sanarwar ta kara da cewa, jirgin na sojojin Malawi ya "bacewa na'urar bin diddigi" bayan ya bar babban birnin kasar, Lilongwe a safiyar ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Alhazan Kano sun samu gata, an fara ciyar da su abinci kyauta a Saudiyya

Jirgin mataimakin shugaban kasar Malawi
Jirgi dauke da mataimakin shugaban kasar Malawi ya bace. Hoto: rbkomar
Asali: Getty Images

Ofishin shugaban kasa da ministocin Malawi ya ce duk wani kokari na tuntubar jirgin daga hukumomin kula da jiragen sama na kasar ya ci tura, in ji rahoton CNN.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jirgin mataimakin shugaban kasa ya bace

Jaridar BBC ta ruwaito mataimakin shugaban kasar ya hau jirgin ne a Lilongwe, babban birnin kasar da misalin karfe 9:00 na safiya kuma har yanzu ba a ganshi ba.

Bisa ga yadda aka tsara tafiyar, jirgin zai sauka babbar tashar jiragen sama ta Mzuzu da misalin karfe 10:00 na safiya, kamar yadda Reuters ta ruwaito.

Sauran fasinjojin da ke cikin jirgin sun hada da matar Mista Chilima, Mary da wasu jami’ai daga jam’iyyar mataimakin shugaban kasar ta United Transformation Movement (UTM).

Saulos Klaus Chilima zai je jana'iza

Bayan da kwamandan rundunar tsaron kasar ya fitar da labarin lamarin, shugaban kasar Malawi, Lazarus Chakwera ya soke tafiyarsa zuwa Bahamas.

Kara karanta wannan

'A rage ciki', An bukaci 'yan majalisa su rage albashinsu domin a samu kudi

Har yanzu ba a san dalilin bacewar jirgin ba, Janar Valentino Phiri ya shaidawa Mista Chakwera.

Mista Chilima dai yana kan hanyarsa zai wakilci gwamnati a wajen jana'izar tsohon minista Ralph Kasambara, wanda ya rasu kwanaki uku da suka gabata.

Jirgin shugaban kasa ya yi hatsari

A wani labarin, mun ruwaito cewa jirgin da ke dauke da shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi a ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian, ya yi hatsari.

Gwamnatin Iran ta ce hatsarin ya hallaka Ebrahim Raisi da mutane takwas, ciki har da ma'aikatan jirgin uku da ke cikin jirgin saman kirar Bell, wanda Iran ta saya a farkon shekarun 2000.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel