An damke dan shekaru 19 dauke da sassan jikin dan adam

An damke dan shekaru 19 dauke da sassan jikin dan adam

An kama wani matashi dan shekaru 19 mai suna Sunday Owo dauke da sassan jikin mutum a wani gidan bayar da maganin gargajiya da ke garin Awka a jihar Anambra da safiyar yau Alhamis.

An kama Owo da sassan al'urar mutum da 'yan yatsun hannu da kuma kwalba cike da jini.

'Yan sanda sun kama matashin ne ta sanadin wata mai bayar da maganin gargajiya mai suna Mrs Ifeanyichukwu Ilonzo wadda ta shaidawa manema labarai cewa Owo dan asalin kauyen Ohaukwu ne a jihar Ebonyi.

Matashin ya ce wata mace mai suna Blessing ne ta umurci ya kawo sassan jikin zuwa gidan bayar da maganin gargajiyar da ke Awka domin ayi masa asirin da zai sa ya yi arziki.

An damke dan shekaru 19 dauke da sassan jikin dan adam
An damke dan shekaru 19 dauke da sassan jikin dan adam
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wani dan majalisa ya sake ficewa daga APC, ya bayar da dalilai

Ya ce ya biya Blessing N50,000 saboda sada shi da gidan bayar da maganin gargajiyar da za ayi masa asirin arzikin.

Owo ya bayyana cewa sassan jikin na wani yaro ne dan shekaru hudu da ya kashe da kansa a garinsu sannan ya jefa kan yaron da sauran sassan jikinsa cikin rafi.

Sai dai Ilonzo, wadda ke da gidan bayar da maganin gargajiyar ta ce akwai wata Blessing Eze da ta zo aka bata maganin kaba amma bata sake dawowa ba.

Ilonzo ta ce wannan ba komai bane illa sharri da ake nufinta da shi, "wannan ba shine karo na farko da ake neman qala min sharri ba har ma kashe ni an nemi yi," inji ta.

Jami'in hulda da jama'a na yan sandan jihar Anambra, SP Mohammed Haruna ya ce an fara gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164