Sabon tsarin harajin VAT ya soma aiki a Najeriya – Inji AGF
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gwamnatin tarayya ta soma dabbaka karin harajin kayan masarufin da ta yi a fadin kasar.
Akanta Janar na kasa, Ahmed Idris, ya bayyana wannan a Ranar Laraba, 15 ga Watan Junairun 2020 a babban birnin tarayya Abuja.
Jaridar ta ce Mista Ahmed Idris ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya zanta da Manema labarai a Garin na Abuja, a jiya da rana.
Daga yanzu bai kamata a rika cirewa kayan masarufin da canjin da aka yi ya shafa harajin 5% ba, bayan an kawo sabuwar doka.
“A jiya na ga wani ciniki da aka yi a Disamban 2019, da mu ka duba sai na ga cewa harajin 5% aka cire, na ce a’a. Kamata ya yi ace harajin 7.5%. aka cire. Wannan ita ce dokar da ke ci.” Inji AGF.
KU KARANTA: Dole mutanen Najeriya su daina zuwa asibitin kasashen waje - Buhari
AGF ya kuma kara tabbatar da niyyar gwamnatin Najeriya na tafiyar da shugabanci na ke-ke-da-ke-ke domin rage satar dukiyar kasa.
Yanzu an kafa wani shafi da ya fara aiki a ofishin babban Akawun gwamnatin Najeriya wanda zai taimaka wajen wannan aiki.
"Mun kuma samu iznin majalisar zartarwa na kafa shafin da kowa na iya bibiya domin ganin abin da gwamnati ta ke batarwa."
"Wannan shafi da aka kirkira zai kuma rika nunawa Duniya abin da duk ya shigo cikin lalitar gwamnati." inji Ahmed Idris.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng