Karin VAT ba zai wani taba Talakan Najeriya ba – Shugaban Majalisa

Karin VAT ba zai wani taba Talakan Najeriya ba – Shugaban Majalisa

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kara kudin harajin wasu kayan masarufi na VAT daga 5% zuwa 7.5. Majalisa ta yi magana game da karin.

Majalisar dattawan kasar ta ba ‘Yan Najeriya tabbacin cewa mutane ba za su wani ji tasirin dabbaka karin sabon tsarin harajin da za yi a kasar ba.

Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya ce wannan kari na 2.5% ba zai yi wa gama-garin ‘Yan Najeriya nauyi wajen sayen kayan da su ka saba amfani da su ba.

Ahmad Ibrahim Lawan ya nuna cewa karin da aka yi zai shafi kayan shakatawa ne da wasu kaya masu tsada, ba wadanda ake bukata a yau da kullum ba.

An rahoto shugaban majalisar kasar ya na cewa: “Karin harajin VAT na 2.5% ba zai shafi kayan da gama-garin ‘Yan Najeriya su ke amfani da su ba.”

KU KARANTA: Aron kudin da Buhari ya ke yi, ya yi yawa Inji Gwamnan CBN

Karin VAT ba zai wani taba Talakan Najeriya ba – Shugaban Majalisa
Lawan ya ce Talaka ba zai karin harajin kayan masarufi ba
Asali: Twitter

“Mafi yawan kayan da aka kara masu haraji da kashi 2.5% na gayu ne wadanda akasarin mutanen kasar ba su amfani da su.” Inji Sanata Ahmad Lawan.

Lawan ya yi wannan jawabi ne a lokacin da aka yi masa tambayoyi game da kokarin da Majalisa ta ke yi domin ragewa al’umma radadin karin harajin.

A Ranar Talata, 28 ga Watan Junairu, 2020, ‘Yan jarida su ka yi wannan hira da Dr. Ahmad Lawan, ganin cewa sabon tsarin harajin ya kusa soma aiki.

A bayanin da ya yi wa Manema labarai, ya nuna masu cewa gwamnati ta na bukatar kudin shiga domin aiwatar da ayyukan more rayuwan da ake bukata.

Kwanan nan ne aka sake jin cewa gwamnatin Najeriya ta na kokawa game da tsarin haraji. Da wadannan kudi ne ake yi wa Talaka abubuwan morewa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel