Karin harajin VAT ba zai shafi burodi, mai, gishiri da wasu kayan gida ba

Karin harajin VAT ba zai shafi burodi, mai, gishiri da wasu kayan gida ba

Bayan suka da jama’a su ke yi game da karin harajin kayan masarufi da aka yi a Najeriya, fadar shugaban kasa ta fito, ta bayyana cewa wannan kari ba zai taba wasu kaya ba.

Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kara yawan kayan da karin VAT da aka yi daga 5% zuwa 7.5% ba zai shafa ba kamar yadda wani jawabi da aka fitar ya nuna.

Mista Laolu Akande wanda ke magana da yawun bakin mataimakin shugaban kasa ya ce babu karin haraji a kan kayan abinci da aka saba amfani da su da kuma irinsu zuma.

A jawabin na sa, Hadimin fadar shugaban kasar ya kuma bayyana cewa sabon harajin ba zai taba burodi, man girki, kifi, fulawa, kayan marmari, danyen nama, da madara ba.

Har ila yau, wannan kari da aka yi na harajin kayan masarufi ba zai taba gyada, gishiri, ruwa da kuma ganye ba. Haka kuma tawul da auduga ko kunzugun mata masu al’ada.

KU KARANTA: An bayyana lokacin da karin harajin da aka yi zai soma aiki

Karin harajin VAT ba zai shafi burodi, mai, gishiri da wasu kayan gida ba
Farashin wasu kaya ba zai tashi a sakamakon karin haraji ba
Asali: Twitter

Wannan jawabi da aka fitar Ranar Lahadi ya kuma nuna cewa 85% na kudin da aka samu daga harajin VAT, za su shiga asusun gwanonin jihohi ne da kuma kananan hukumomi.

A cewar mataimakin shugaban kasar, za ayi amfani da wadannan kudi wajen gina abubuwan more rayuwa. An fitar da wannan jawabi ne a Ranar Lahadi20 ga Watan Junairu, 2020.

Akande ya kuma bayyana cewa har yanzu Najeriya ta na cikin inda ta fi ko ina arahar VAT a Duniya, sannan kuma duk Afrika babu kasar da ta sha gaban ta wajen saukin VAT.

Fadar shugaban kasar ta kuma yi bayani game da canjin da aka yi wa harajin CIT inda za a daina karbar haraji wajen kananan kamfanoni tare da rage harajin da aka saba karba a da.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng