N11,000/50kg: Hauhawar Farashin Siminti da Matsalolin da Yake Haifarwa a Najeriya

N11,000/50kg: Hauhawar Farashin Siminti da Matsalolin da Yake Haifarwa a Najeriya

  • Hauwar farashin siminti ya kara jawo tsadar gine-gine, wanda kuma ya zama kalubale ga 'yan Najeriya da ke muradin mallakar gidaje
  • Wasu daga cikin dalilan hawan farashin sun hada da faduwar Naira, karancin sarrafa simintin, tsadar fetur da makamashi da sauransu
  • Abdullahi Rabiu, da Legit Hausa ta zanta da shi, ya koka kan yadda tsadar siminiti da kayan gine-gine suka zama baranaza ga kamfanoni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

A cikin 2024, farashin siminti a Najeriya ya yi tashin gwauron zabi, abin da ya ba 'yan kasuwa da kwastomomi da dama mamaki.

Business Day ta ruwaito cewa farashin buhun siminti ya tashi daga Naira 8,000 zuwa Naira 11,000, duk kuwa da matakin da gwamnatin tarayya ta gindaya a baya a kokarin rage farashin.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da fursuna ya karbe bindigar jami'i, ya harbe wani mutum

Wannan fuju'ar tashin farashin simintin ya kawo cikas ga gine-gine kuma ya yi tasiri mai yawa a sassa da yawa na kasar, musamman talakan da ke son mallakar gidaje.

Tsadar farashin siminti a Najeriya
Kamfanonin da ke dogaro da siminti na fuskantar durkushewa wanda zai jawo mutane su rasa ayyukan yi. Hoto: Afrik 21, The Hindu Business line
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana fuskantar kalubale na tsadar siminti

Ayyukan gine-ginen gwamnati da ake yi domin bunkasa abubuwan more rayuwa, yanzu suna fuskantar barazana daga ƙarin farashin siminitin, mai yuwuwar a dakatar da wasu ayyukan.

Rahoton Tribune Online ya yi nuni kan yadda hauhawar farashin simintin ke zama barazana ga masu karamin karfi.da ke kokarin mallakar gidaje.

Kamfanonin da ke dogaro da siminti wajen gine-gine yanzu suna fuskantar kalubale, wanda zai iya haifar da durkushewar wasu da jawo rasa ayyukan mutane da dama.

Kamfanoni da bambancin farashin siminti

A Najeriya, akwai bambancin farashin siminti mai nauyin 50kg da kamfanonin siminti ke bayar wa.

Shahararrun kamfanoni kamar Dangote, Lafarge, Ibeto, BUA, da UNICEM suna da tsarin farashi iri ɗaya.

Kara karanta wannan

"Mijina ya daina kwana da ni a gado" Matar aure ta cire kunya ta fashe da kuka a kotu

Simintin Ibeto da BUA sune mafi araha, sai Dangote a matsakaicin farashi, tare da simintin UNICEM da Lafarge da ya fi tsada.

Sauyawar farashin siminti a Najeriya

Sauyawar farashin siminti a Najeriya, daidai da kasuwannin duniya, ya samo asali ne daga abubuwa da dama da ke da alaka da juna.

1. Faduwar Naira a kasuwa

La'akari da cewa Najeriya ta dogara da shigo da kayayyakin sarrafa kayan gini daga kasashen waje, faduwar Naira ya yi tasiri sosai kan farashin shigo da kayan, wanda hakan ya shafi farashin siminti.

Shafin ResearchGate ya alamta cewa idan har darajar dalar Amurka ta ci gaba da haurawa sama, kudaden da ake kashewa wajen shigo da kayayyaki za su cigaba da karuwa, wanda zai tilasta kara farashin simintin.

2. Tsadar mai da gas

Nauyi da yawan adadin buhun siminti na daga abubuwan da ake la'akari da su wajen kayyade farashin sayar da siminiti, sakamakon kuɗin sufurin kayan da za a kashe.

Kara karanta wannan

Daliban jami'a 4 sun lakadawa abokin karatunsu duka har ya mutu, ‘yan sanda sun dauki mataki

Tsadar fetur da iskar gas da motoci ke amfani da su wajen sufurin simintin ya taimaka wajen hauhawar farashin kayan ga masu saye domin amfani da shi kai tsaye.

3. Tsadar kayan sarrafa wa

Samar da siminti ya dogara kan abubuwa kamar dutsen farar ƙasa, yumbu, gypsum, da man fetur, waɗanda tsadar farashinsu zai iya jawo tsadar farashin siminti gabaɗaya.

Idan kudin sayen kayan sarrafa simintin suka karu, zai zama wajibi ga masana'antun siminti su sake daidaita farashin domin ba za su yi asara ba.

4. Samuwar simintin da yawan masu nema

Farashin siminti a Najeriya yana ta'allaka ne akan yanayin kasuwar buƙata da karfin samuwarsa a kasuwa.

Idan aka samu karuwar buƙatar simintin don gudanar da ayyukan gine-gine amma kuma akwai karancinsa a kasuwa, yana yana haifar da hauhawar farashin simintin.

5. Tsare-tsaren gwamnati da haraji

Dokokin gwamnati, harajin shigo da kayayyaki, da harajin da aka sanya akan samar da siminti da sayar da shi na taka muhimmiyar rawa wajen hauhawar farashin siminti a Najeriya.

Kara karanta wannan

CBN ya dauki mataki mai karfi domin farfado da darajar Naira a kan Dalar Amurka

6. Farashin Makamashi

Idan ana maganar samar da siminti, to makamashi ya na zama babban ginshiki ga masana'antar siminti gaba daya, kamar dai ace da bazarsa ake taka rawa.

Rashin daidaito a farashin makamashi na iya yin tasiri kai tsaye akan farashin samar da simintin, wanda zai iya haifar da kara farashin siminti don maye gurbin karin kudin makamashin.

An nemi gwamnati ta rage farashin siminti

A zantawarsa da Legit Hausa, Abdullahi Rabiu, wani mai aikin zane da gina gidaje a Abuja, ya bayyana damuwarsa kan yadda tsadar siminti ke kokarin nakasa masana'antar gine-gine.

Rabiu ya buga misali da cewa, idan a 2022 Naira miliyan 50 za ta gina babban gida mai dakuna 5, yanzu a 2023/2024, naira miliyan 100 ba lallai ta iya gina shi ba.

"Akwai aikin wani rukunin gidaje da muke yi a nan Abuja, rukuni 4 ne, amma daga 2021 zuwa 2022 mun kammala rukuni biyu, daga 2023 zuwa yau da nake magana, mun kashe kudaden da muka gina rukunoni biyu din farko wajen gina rukuni daya.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar na ba da tallafin naira 100,000? An bankado shirin wasu mazambata

"An samu tashin farashin siminti, fetur, kudin sayo manyan motocin aiki, tsadar kudin gas, kudin kwanon rufi, katako, rodi, da ma kudin 'yan aiki, komai fa ya nunka farashinsa sau biyu ko uku."

Kamfanonin gine-gine na durkushewa

Rabiu ya roki gwamnati da ta dawo da biyan tallafin fetur, ta bude iyakokin kasa, ko kuma ta dauki wasu matakan don ganin farashin siminti da kayan gini sun sauka a kasar.

Ya yi nuni da cewa akwai kananun kamfanonin gine-gine a Abuja da yanzu sun hakura da nemo kwangila, saboda tsoron yin asara idan aka samu akasi farashi ya karu akan wanda suka yi yarjejeniya da kwastoma.

Legas: Farashin siminti ya koma N11,000

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa farashin siminiti ya haura zuwa N11,000 a kan kowanne buhu daya a wasu sassa na jihar Legas.

W!annan na zuwa ne yayin da gwamnati da kamfanonin sarrafa simintin suka kulla wata yarjejeniyar na rage kudin simintin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel