Sallah: Buhari Ya Fadi Hanya 1 da 'Yan Najeriya Za Su Samu Sauki, Ya Tura Sako

Sallah: Buhari Ya Fadi Hanya 1 da 'Yan Najeriya Za Su Samu Sauki, Ya Tura Sako

  • Yayin da ake ci gaba da bukukuwan salla karama, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya taya al'ummar Musulmai murna
  • Buhari ya bayyana cewa hadin kai da goyon baya ga shugabanni ne kadai zai kawo ci gaba a kasar musamman a wannan yanayi
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da tsohon shugaban ya wallafa a shafinsa na X a yau Laraba 10 ga watan Afrilu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya taya al'ummar Musulmai murnan sallar azumi.

Buhari ya shawarci 'yan kasar da su goyawa shugabanni baya domin samun ci gaba a kasar.

Kara karanta wannan

Sallah: Kungiyar CAN ta tura sako mai kama hankali ga al'ummar Musulmai a Najeriya

Buhari ya taya al'ummar Musulmai murnan bikin salla, ya shawarce su
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya taya Musulmai murnan bikin salla. Hoto: Muhammadu Buhari.
Asali: Getty Images

Wace shawara Buhari ya ba 'yan Najeriya?

Ya ce goyon bayan shugabanni ne kadai zai inganta kasar musamman a wannan yanayi da ake ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari ya bayyana haka ne a shafinsa na X a yau Laraba 10 ga watan Afrilu yayin murnan bikin salla.

"Goyon bayan shugabanni da hadin kai a Najeriya shi ne zai kara inganta kasar."
"Ya na da matukar muhimmanci a hada kai domin kare martabar Najeriya da kuma inganta ts."

- Muhammadu Buhari

Buhari ya yi godiya ga al'ummar Daura

Buhari ya kuma shawarci 'yan siyasa da su yi siyasa mai inganci ba tare da ta da hankulan al'umma bahsr zuwa karshen wa'adinsu na mulki.

Ya godewa al'ummar Daura da ma jihar Katsina baki daya kan irin tarbar da suka yi masa yayin sallar idin.

Har ila yau, Buhari ya nuna jin dadinsa ganin yadda yake cikin al'ummarsa tsundum bayan kammala wa'adinsa a matsayin shugaban kasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya aika sako, ya taya Kanawa murnar kammala azumin Ramadan

Buhari ya jajanta kan rasuwar Ali Chiroma

A baya, mun kawo muku labarin cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tura sakon jaje kan rasuwar Ali Chiroma a jihar Borno.

Chiroma shi ne tsohon shugaban kungiyar kwadago ta NLC wanda ya rike mukamin fiye da shekaru 30 da suka wuce a Najeriya.

Buhari ya bayyana marigayin a matsayin shugaba marar tsoro kuma mai tsantseni kan harkokin rayuwa wanda ya ba da gudunmawa wurin inganta tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel