Neja: An Shiga Fargaba Bayan 'Yan Bindiga Sun Sake Hallaka Sojoji Tare da Sace Kyaftin

Neja: An Shiga Fargaba Bayan 'Yan Bindiga Sun Sake Hallaka Sojoji Tare da Sace Kyaftin

  • Sojoji sun sake tafka babban rashi bayan kisan wasu sojoji shida da 'yan bindiga suka yi a jihar Neja da ke Arewacin Najeriya
  • Yayin harin da ya yi ajalin sojojin, maharan sun kuma yi garkuwa da wani Kyaftin din soja a kauyen Roro da ke jihar a ranar Juma'a
  • Kwamishinan tsaron cikin gida a jihar Neja, Burgediya-janar Bello Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin ga 'yan jaridu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Niger - 'Yan bindiga sun kai samame tare da hallaka sojoji shida a wani sabon hari a jihar Neja.

Lamarin ya faru ne a Karaga da Rumace a yankin Bassa da ke karamar hukumar Shiroro a jihar a daren Juma'a 19 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Jirgin sojoji ya kuma 'kashe' mutane ana shirin sallar idi a kauyen Zamfara

Yan bindiga sun yi ajalin sojoji tare da sace Kyaftin din soja
Aƙalla sojoji 6 ne suka mutu yayin wani hari da 'yan bindiga suka kai a jihar Neja. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Twitter

Yadda aka yi ajalin sojojin a Neja

Daily Trust ta tattaro cewa sojojin sun gamu da ajalinsu ne yayin kai wani dauki inda maharan suka far musu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin harin har ila yau, maharan sun yi garkuwa da wani soja mai girman Kyaftin yayin da suka farmaki sojojin a kauyen Roro.

Duk da wannan ta'asa da suka yi, sun kuma hallaka wani mai farauta da manoma biyu tare da kona gidaje da abinci a yankin.

Martanin wasu mazauna yankin kan lamarin

Wasu mazauna yankin sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:00 na daren Juma'a 19 ga watan Afrilu.

Wani mazaunin yankin, Mustapha Bassa ya ce maharan sun zo ne a kan babura inda suka yi ta harbi sama yayin da suke shiga cikin kauyen.

Har zuwa yanzu rundunar sojojin Najeriya ba ta yi martani kan lamarin ba bayan tuntubarsu da 'yan jaridu suka yi.

Kara karanta wannan

Kwamishinoni sun ba hammata iska a taron karbar sababbin tuba daga PDP zuwa APC

Sai dai kwamishinan tsaron cikin gida a Neja, Burgediya-janar Bello Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin ta sakon karta-kwana.

Sojoji sun kama jami'ansu kan sata

A wani labarin, rundunar sojoji ta yi nasarar cafke jami'anta guda biyu da zargin sata a matatar man Aliko Dangote da ke Legas.

Rundunar ta yi Allah wadai da wannan aika-aika da sojojin suka yi inda ta yi alkawarin bincike da kuma daukar mataki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel