Ana Fuskantar Barazanar Kwantai, Neman Masu Sayen Danyen Man Najeriya Yayi Wahala

Ana Fuskantar Barazanar Kwantai, Neman Masu Sayen Danyen Man Najeriya Yayi Wahala

  • Dalilai da yawa sun jawowa Najeriya matsala a kasuwar duniya, an rasa wadanda za a saidawa danyen man da aka fitar
  • Faransa da ta saba sayen mai a hannun Najeriya ta ja baya domin zanga-zangar da ake yi ya yi sanadiyyar rage shan mai
  • Wasu kasashe sun yi watsi da man kasar nan saboda tsada yayin da ake gyaran mafi yawan manyan matatun da ke Turai

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Najeriya tana shan wahala wajen samun masu sayen danyen mai a kasuwar duniya wanda hakan yana iya zama matsala.

Najeriya ta dogara ne da danyen arzikin mai wajen samun kudin shiga. A halin yanzu kasar na fuskantar matsin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Kano: An shiga fargaba yayin da gungun matasa suka hallaka wani almajiri ɗan shekaru 16

Man Najeriya
Danyen man Najeriya yana jibge a kasuwannin Turai Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Masu sayen mai a Turai sun ragu

Daga rahoton Bloomberg aka fahimci cewa wadanda ke neman mai a kasuwa sun ragu saboda yajin-aiki da ake yi a kasar Faransa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baya ga haka, gyare-gyare da ake yi a matatun man Turai ya taimaka wajen wannan matsala za ta iya shafen har kasafin kudin 2024.

Manyan ‘yan kasuwan da suka saba sayen mai a hannun kasashen Afrika ta yamma sun ce akwai jirage 20 zuwa 25 da ba a saya ba.

Danyen man Najeriya suna ajiye

Kowane jirgi yana dauke da kusan ganga miliyan daya na danyen mai, amma har yanzu suna jibge ba tare da an samu mai saye ba.

Rahoton ya nuna a kowace rana, kasar Faransa ta na sayen ganguna 110, 000 na danyen mai daga Najeriya, an fi shekara guda a haka.

Kara karanta wannan

Mun dauki matakan saukar da farashin gas, cewar ministan mai

Faransa tana cikin kasashen da suka fi kowane sayen mai daga hannun Najeriya a yau.

Faransa ta rage shan man Najeriya

Jaridar The Cable ta ce ana zanga-zanga a Faransa saboda garambawul da gwamnatin kasar ta ke kokarin yi wa dokokin Fansho.

An rage rububin danyen mai saboda gyaren manyan matatun kamar Pernis na Shell Plc da San Roque na Sifen da Sarroch da ke kasar Italiya.

Sannan kasashen Indiya da Indonesiya sun koma sayen mai daga hannun wasu kasashen saboda ana ganin sun fi araha yanzu a kasuwa.

Dala tana karyewa a kan Naira

Wani rahoto mai dadi ya ce zuwa karshen shekarar 2024, masana sun yi hasashen Dala za ta kara karyewa a kasuwannin canjin kudi.

Idan aka biyewa hasashen Goldman Sachs Group Inc, sai an saye Dalar Amurka a kasa da N1, 000 alhali wasu na jiran Dalar ta tashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel