NAPTIP ta damke budurwa da ta tura 'yan uwanta 3 karuwanci

NAPTIP ta damke budurwa da ta tura 'yan uwanta 3 karuwanci

Hukumar yaki da safarar mutane ta jihar Edo (NAPTIP) ta kama tare da gurfanar da wata budurwa mai shekaru 28 mai suna Vivian Francis sakamakon jan 'yan uwanta uku da tayi daga Cross River zuwa Benin City karuwanci.

A takardar da kwamandan NAPTIP ta yankin, Ijeoma Uduak ta fitar, ta ce Vivian ta ja kannanta masu shekaru 15, 17 da 18 zuwa Benin City da zummar za ta samar musu aiki.

Kamar yadda Uduak ta bayyana, an kama Vivian a wani fitaccen otal ne a yayin kullen COVID-19 kuma ta amsa laifinta wanda abun hukuntawa ne a sashe na 13 na dokokin NAPTIP.

Uduak ta ce an gurfanar da Vivian a gaban Mai shari'a Isoken Erameh na babbar kotun jihar inda ta amsa laifinta.

An yanke mata hukuncin shekara daya a gidan gyaran hali ko kuma tarar N125,000 a matsayin wacce aka gurfanar a karon farko.

"Mun kama mai laifin a yayin kullen COVID-19 a wani fitaccen otal da ke Benin. Ta amsa laifinta na cewa ta je jihar Cross River inda ta kwaso kanninta masu shekaru 15, 17 da 18.

NAPTIP ta damke budurwa da ta tura 'yan uwanta 3 karuwanci
NAPTIP ta damke budurwa da ta tura 'yan uwanta 3 karuwanci. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Daga karshe: FG ta yi magana a kan bude makarantun gaba da sakandare

"Ta ce za ta samar musu da aikin yi amma bayan isowarsu Benin, sai ta sa su karuwanci tare da karbar kudin.

"An damketa tare da gurfanar da ita. Bayan amsa laifin da tayi an yanke mata hukunci." Takardar tace.

Uduak ta kara da cewa an mika 'yam matan ga danginsu a jihar Cross River.

A lokacin da aka nemi jin ta bakin Vivian, ta ce ta yi nadamar laifin da ta aikata.

A wani labari na daban, wani mutum mai matsakaicin shekaru mai suna Babangida Eluemuno, ya shiga hannun 'yan sanda bayan ya kashe wata 'yar kasuwa a gidansa da ke lamba 9, titin Agba da ke garin Onitsha a jihar Anambra.

Marigayiyar mai suna Arinze Omeh, matashiya ce daga Enugwu-Ezike a karamar hukumar Igbo-Eze ta jihar Enugu.

A yayin bayyana yadda abun ya faru, Oluchukwu Omeh, dan uwan Arinze, ya sanar da manema labarai cewa a ranar Talata ne rigimar ta barke tsakanin 'yar uwarsa da dan mai gidan hayar da suke.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel