Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya nada Hajia Imaan Suleiman babbar diraktar hukumar NAPTIP

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya nada Hajia Imaan Suleiman babbar diraktar hukumar NAPTIP

- Shugaban kasa ya yi nadi mai muhimmanci a ma'aikatar hana safarar mutane

- Najeriya na fama da matsalan safarar mutane zuwa kasashen waje domin bauta da karuwanci

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim a matsayin sabuwar shugabar hukumar dakile mutane watau NAPTIP.

Shugaban ya bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu.

Ya bayyana cewa gabanin nadinta ta kasance babbar mai bada shawara ga Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, kan sadarwa.

Imaan za ta maye gurbin Julie Okah-Donli wacce Buhari ya nada tun shekarar 2017.

Yace: "Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Imaan Sulaiman-Ibrahim matsayin sabuwar dirakta janar na hukumar NAPTIP."

"Mrs Sulaiman Ibrahim 'yar asalin jihar Nasarawa ce kuma ta karanci Sociology a jami'a sanan tayi digir-gir a kasuwanci."

KU KARANTA: Za'a dawo da Abdulrashid Maina Najeriya daga Nijar, Hukumar yan sanda

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya nada Hajia Imaan Suleiman babbar diraktar hukumar NAPTIP
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya nada Hajia Imaan Suleiman babbar diraktar hukumar NAPTIP Hoto: Iman Suleiman-Ibrahim
Source: Facebook

KU DUBA: Kisan manoma 73 a Zabarmari: Sheikh Ahmad Gumi ya aike wa Buhari muhimmin sako

A bangare guda, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Talata, ya bayar da umarnin sakin sabbin manyan motocin alfarma domin saukakawa jama'a kalubalen sufuri da rage musu radadin kara farashin man fetur.

Buhari ya mika sakon godiyarsa ga 'yan Najeriya bisa abin da ya kira 'hakurin da suka nuna' dangane da kalubalen tattalin arziki da kasa ke fuskanta

Kazalika, ya godewa mambobin kungiyar kwadago bisa fahimta da dattakon da kuma kishin kasa da suka nuna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel