Farashin Kayayyaki Ya Fara Sauka Yayin da Naira Ke Ci Gaba da Yin Daraja

Farashin Kayayyaki Ya Fara Sauka Yayin da Naira Ke Ci Gaba da Yin Daraja

  • Farashin wasu kayayyaki kamar shinkafa, sukari, fulawa, taliyar indomi da dai sauran su ya fara sauka a kasuwannin Najeriya
  • Wannan kuwa ya faru ne sakamakon darajar da Naira ta yi a kan Dalar Amurka da ma sauran kudaden kasashen waje
  • Kamfanin harkar kudi na Derivatives Limited ya ce farashin kayayyaki zai ci gaba da faduwa yayin da Naira ta ke kara daraja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Farfadowar darajar Naira a kan dala da sauran kudaden duniya ya jawo faduwar farashin wasu kayayyaki a Najeriya.

Farashin kayayyaki ya fara sauka yayin da Naira ta kara yin daraja
Farashin wasu kayayyaki kamar shinkafa, sukari, fulawa, taliyar indomi ya sauka. Hoto: Emmanuel Osodi/Anadolu Agency
Asali: Getty Images

Darajar Naira da farashin kayayyaki

Rahoton mujallar Bloomberg ya nuna cewa tattalin arzikin Najeriya zai habaka yayin da farashin kayayyaki zai ci gaba da faduwa idan Naira ta ci gaba da yin daraja.

Kara karanta wannan

Crypto: Yayin da darajar BTC ta fadi zuwa $62,000, wani matashi ya tafka asarar N1.3bn

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shi ma shugaban kamfanin kamfanin harkar kudi na Derivatives Limited, Bismarck Rewane ya ce karfin da Naira za ta samu a yanzu shi zai yanke farashin kayan masarufi nan gaba.

Bismarck Rewane, ya ce Naira a kasuwannin gwamnati da na bayan fage suna sayar da hada-hadar kudin a kan N1,260/$ da kuma N1,125/$, jaridar The Nation ta ruwaito.

"Farashin shinkafa, sukari ya sauka" - Rewane

Kamar dai yadda aka yi hasashe, farashin wasu kayan abinci ya fara sauka dai dai da ci gaban darajar da Naira ke samu.

“Musamman farashin wasu kayayyaki kamar shinkafa (50kg) ya ragu da kashi 5.26 zuwa N90,000/buhu, sukari ya fadi da kashi 5.88 zuwa N80,000/buhu.
"Garin fulawa ya samu raguwar kashi 7.81 zuwa N59,000/buhu, sannan taliyar indomi ta ragu da kashi 15.22 bisa dari zuwa N7,800/kwali.”

Kara karanta wannan

Akwai dalili: Shekara 1 na Shugaba Tinubu ta fi shekaru 8 na mulkin Manjo Buhari, Reno Omokri

- A cewar Rewane.

Rewane ya bayyana cewa yayin da wasu ‘yan kasuwa suka fara samun sababbin kayansu, da akwai yiwuwar farashin zai kara sauka kwatankwacin darajar Naira.

Dabarun CBN na farfado da Naira

A baya Legit Hausa ta ruwaito cewa babban bankin Najeriya (CBN) a baya-bayan nan ya aiwatar da wasu tsare-tsare na tsaftace kasuwar musayar kudaden waje (FX).

Wannan matakin zai dora Naira a kan turbar farfadowa tun bayan da ta yi kololuwar faduwa zuwa N1,915/$ a cikin watan Fabrairu.

Hakanan Naira ta samu karfin farfadowa bayan da CBN ya biya dukkanin basussukan kudaden waje da kuma dawo da sayar da daloli ga 'yan kasuwar BDCs.

Asali: Legit.ng

Online view pixel