'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Ɗalibai Masu Ɗimbin Yawa a Jihar Arewa, Gwamna Ya Magantu

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Ɗalibai Masu Ɗimbin Yawa a Jihar Arewa, Gwamna Ya Magantu

  • Malam Dikko Radda ya ce akwai bukatar samar da tsaro a makarantu domin magance sace-sacen ɗaliban da aka yi a baya a Katsina
  • Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya jagoranci tawaga zuwa ofishin TETFUND a birnin tarayya Abuja
  • Dikko ya ce Katsina na fuskantar barazanar tsaro kuma kuɗin shigar da take samu ba zasu isa ta magance matsalolin da suka dabaibayeta ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda, ya ce an yi garkuwa da dalibai da dama daga makarantu daban-daban na jihar da ke Arewa maso Yamma.

Gwamnan ya bayyana cewa babu tababa jiharsa Katsina tana fuskantar babbar barazanar tsaro, kamar yadda jaridar Vanguard ta tattaro.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnan Arewa ya sharewa iyalai 70,000 hawaye, ya raba kayan abinci na miliyan 225

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda.
An sace ɗalibai da yawa daga makarantun jihar Katsina, Gwamna Radda ya koka Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda Ph.D
Asali: Twitter

Dakta Radda ya ƙara da cewa makarantu, musamman jami'o'i da sauran manyan makarantun gaba da sakandire na buƙatar isasshen tsaro domin ɗalibai su samu nagartaccen ilimi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dikko ya kai ziyara TETFUND?

Bisa haka, gwamnan ya yi kira ga asusun tallafawa manyan makarantu (TETFUND) da ya taimaka wajen magance matsalolin rashin tsaro da ke addabar manyan makarantun Katsina.

Malam Raɗɗa ya yi wannan furucin ne yayin da ya jagoranci tawagar jami'an gwamnatinsa suka kai ziyara TETFUND a birnin Abuja.

Ya ce ƴan ta'adda sun yi garkuwa da ɗalibai da dama a lokuta daban-daban saboda haka jihar na bukatar tallafi domin samar da kayan more rayuwa ga ɗalibai.

A rahoton Tribune, Gwamna Raɗɗa ya ce:

"Ya zama dole mu yabawa gwamnatin tarayya bisa ayyukan da take yi, bamu san ya makarantun mu zasu kasance ba idan babu TETFUND. Jihohi na fama, kasa na fama da matsalar matsin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya faɗi hanyar da mutane zasu bi su Kare kansu daga hare-haren ƴan bindiga

"Arewacin Najeriya na fama da matsalar tsaro kuma kuɗin da muke samu ba zasu isa mu magance waɗannan kalubale ba, don haka TETFUND wuri ne da zamu zo neman agaji.
"Muna fuskantar barazanar tsaro kuma an sace ɗalibai da dama a baya, saboda haka muna bukatar samar da tsaro a makarantu domin ɗalibai su samu damar karatu ingantacce."

Yan bindiga sun kashe ƴan kasuwa 9

A wani rahoton kuma Yan bindiga sun halaka ƴan kasuwa 9 a kan hanyar komawa gida bayan tashi daga kasuwar Jibia ranar Lahadi da yamma.

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun kuma ƙona motoci biyu da ƴan kasuwar ke ciki kuma ana zargin sun yi garkuwa da wasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel