Fusatattun Yarbawa Na Son a Raba Najeriya, Sun Farmaki Sakateriyar Gwamnati a Oyo

Fusatattun Yarbawa Na Son a Raba Najeriya, Sun Farmaki Sakateriyar Gwamnati a Oyo

  • Bidiyo ya nuna yadda aka kama wasu tsageru da ke kokarin kai farmaki a sakateriyar gwamnatin jihar Oyo
  • Rahoto ya bayyana cewa, sun mamaye wurare sama da uku a jihar, inda suke harba bindigogi ba kakkautawa
  • Ya zuwa yanzu, rahoto ya bayyana halin da ake ciki da kuma matakin da ake ci gaba da dauka a hukumance

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Oyo - Wasu tsageru da ake fargabar 'yan fafutukar kafa kasar Yarbawa ta Odudua ne sun kai farmaki a sakateriyar gwamnatin jihar Oyo.

Tsagerun da suka dura sakateriyar da makamai sun mamaye sakateriyar ne a shirinsu na aikata barnar da ba a yi tsammani ba.

Kara karanta wannan

Hotunan yadda ’yan sanda suka kwamushe ’yan daba 61 da ke tada zaune tsaye a jihar Kano

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, wasu daga tsagerun sun mamaye mashiga ofishin gwamnan jihar, inda wasu kuma suka mamaye majalisar dokokin jihar.

Yarbawa sun farmaki gwamnatin Oyo
Yadda 'yan awaren Yarbawa suka farmaki Oyo | Hoto: Abdul_A_Bello, @seyimakinde
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kame wasu daga cikin 'yan awaren

Wannan lamari dai ya tada hankali a jihar, inda jami'an tsaro da dama suka yi kokarin shawo kan lamarin don wanzar da zaman lafiya.

A wani bidiyon da wakilin Legit ya gani a shagin Twitter na Oyo Affairs, an ga lokacin da 'yan sanda suka kame wasu daga cikin 'yan daban.

An ga tsagerun sanye da wani nau'ikin kakin soja da ke nuna alamar sun dauki makamai ne don yakar gwamnati.

Kalli bidiyon:

Yadda matsalolin aware suke a Najeriya

Majiya ta bayyana cewa, a halin da ake ciki wasu da dama sun kauracewa bin titunan da lamarin ya faru.

Fafutukar kafa kasar Yarbawa na da alaka da wani mai rajin kare hakkin Yarbawa, Sunday Igboho, wanda gwamnati ke takun saka da shi.

Kara karanta wannan

Kano: An shiga fargaba yayin da gungun matasa suka hallaka wani almajiri ɗan shekaru 16

Baya ga Yarbawa, 'yan awaren Igbo, su Nnamdi Kanu da 'yan tsaginsa na Biafra na ci gaba da matsin lamba kan raba Najeriya.

An kama 'yan daba a Kano

A jihar Kano kuma, kun ji yadda aka kame wasu 'yan daba da ke kokarin tada zaune tsaye a lokacin bikin sallah.

Wannan lamari ya kai ga kame mutane samda 60, inda aka hada suka cika 115 a hannun 'yan sanda yanzu haka.

Jihohin Najeriya na fama da rashin tsaro, lamarin da ke kara sanya fargaba a zukatan 'yan kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel