Innalillahi: Tsohon Dan Majalisar Wakilai Ya Yanki Jiki Ya Fadi Bayan Dawowa Daga Sallar Idi a Abuja

Innalillahi: Tsohon Dan Majalisar Wakilai Ya Yanki Jiki Ya Fadi Bayan Dawowa Daga Sallar Idi a Abuja

  • Rahotanni na tsohon dan Majalisar Tarayya, Mohammed Ibrahim Idris ya yanki jiki ya fadi bayan ya dawo daga sallar Idi
  • Tuni aka yi sallar jana'izar sa a makabartar dake Gudu s birnin Tarayya Abuja kamar addinin Musulunci ya koyar
  • Marigayin ya wakilci yankin shi a majalisar wakilai lokacin da mahaifinsa ke mulkin jihar Kogi da ke Arewacin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kogi - Mohammed Ibrahim Idris, tsohon dan majalisar wakilai kuma dan tsohon gwamnan jihar Kogi, Ibrahim Idris, ya rasu a yau Laraba a Abuja.

Ibrahim Idris
Tinin anyi janazar shi a Abuja Hoto: Leadership
Asali: Facebook

Jaridar PM News ta ruwaito cewa ya yanki jiki ya fadi ne bayan sallar idi a gidansa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Bikin Sallah: Wurare 5 masu kayatarwa da ya kamata ku ziyarta a Kaduna

Cikin juyayi aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a makabartar Gudu da ke Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani rahoto kuma da jaridar leadership ta wallafa, Mohammed ya taba wakiltar mazabar Ankpa da Olamaboro da kuma Omala na jihar Kogi a majalisar wakilai a lokacin mahaifinsa yana gwamnan jihar.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba'a samu bayani daga 'yan uwan marigayin ko ma'aikatan lafiya akan dalilin mutuwar ta shi ba.

Babban basarake a Legas ya rasu

Kun ji cewa an shiga jimami bayan rasuwar Osolo na masarautar Isolo a jihar Legas, Oba Kabiru Agbabiaka, ya na da shekaru 64.

Rahotanni sun tabbatar da cewa basaraken ya rasu ne a ranar Laraba 10 ga watan Afrilu a Legas jim kadan bayan dawowa daga sallar Idi.

Kara karanta wannan

Yadda aka shiga tsakani don sulhunta Dr. Idris Dutsen Tanshi da abokan dambarwarsa

Shugaban karamar hukumar Isolo a jihar Legas, Olasoju Adebayo shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba 10 ga watan Afrilu.

Jarumar Kannywood ta rasu

Har ila yau, kun ji cewa Allah ya yi wa shahararriyar jarumar masana'antar fina-finai ta Kannywood, Saratu Gidado Daso rasuwa.

Marigayiyar ta rasu ne da sanyin safiyar ranar Talata, 9 ga watan Afirilun 2024 bayan ta kammala sahur.

Daso wacce ta rasu tana da shekara 56 an haife ta ne a ranar 17 ga watan Janairu, 1968 a cikin birnin Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel