An Yi Jana'izar Mutumin da Aka Kashe Bisa Zargin Ya Yi Batanci a Jihar Sokoto

An Yi Jana'izar Mutumin da Aka Kashe Bisa Zargin Ya Yi Batanci a Jihar Sokoto

  • An yi jana'izar mahaucin nan da mutane suka kashe bisa zargin ya yi ɓatanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW a Sakkwato
  • Waɗanda abun ya auku a kan idonsu sun tabbatar da cewa yadda mutane ke yayata lamarin ba haka ne ya faru ba
  • Ganau ya ce mamacin ba ɓatanci ya yi wa manzon Allah SAW ba, hasali ma gyara ya yi wa almajiri mai neman taimako

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Sokoto - Hawaye sun kwaranya a wurin jana'izar marigayi Usman Buba, mahauci kuma mahaddacin Alƙur'ani wanda aka kashe bisa zargin ɓatanci ranar Lahadi a Sakkwato.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa an ɓinne Usman bayan masa Sallar Janaza kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada a Masallacin Jumu'a da ke Mabera da karfe 2:30 na ranar Talata.

Wurin da aka yi jana'izar Usman a Sakkwato.
An Yi Jana'izar Mutamin da Aka Kashe Bisa Zargin Ya Yi Batanci a Jihar Sokoto Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Sheikh Musa Lukuwa ne ya jagoranci yi wa marigayin Sallar Janaza kuma bayan haka aka ki shi makwancinsa.

Kara karanta wannan

Dan Majalisa Mafi Karancin Shekaru: Yadda Rasuwar Yayana Ya Yi Sanadin Shiga Ta Siyasa

Menene gaskiyar abinda ya faru?

Dandazon jama'a ne suka tararwa Usman Buba da duka da sukar wuƙa har ya rasa rayuwarsa bayan wata gardamar aƙida ta shiga tsakani a babbar mahautar Sakkwato.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan kisan da aka yi wa bawan Allah ya bar baya da ƙura yayin da shaidun da aka yi komai a gabansu, suka ƙaryata zargin cewa ya yi wa Annabi SAW ɓatanci.

Ɗaya daga cikin ganau, Nuhu Bala, ya ce ko kaɗan Usman bai yi kalaman ɓatanci ga fiyyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) ba kamar yadda makasan suka yi iƙirari.

"Abinda ya faru Usman na yi wa wani Almajiri nasiha ne kan cewa ba'a amfani da sunan Manzon Allah wajen neman taimako. Nan wasu abokan sana'arsa da basu fahimce shi ba suka fara kiransa da kafiri."
"Suka fara ihun ai ya ci mutuncin fiyayyen halitta ya yi kalaman ɓatanci ga Annabi SAW, suka fara jifansa da duwatsu, suna caka masa wuƙake."

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Bayani, Sharuda da Ka’idojin da Ya Kamata Duk Mai Layyah Ya Kiyaye

"Da farko mun yi kokarin ƙwatarsa muka zagaye shi amma suka ci ƙarfin mu, mun yi hanzarin faɗa wa 'yan sanda amma kafin su zo an riga an kashe shi."

Kada Ku Ci Bashin Ragon Layya, Malamin Addini Ya Gargadi Al'ummar Musulmi

A.wani labarin na daban kuma Fitaccen malamin addinin Musulunci ya yi gargadi ga al'ummar Musulmi kan runtumo bashi don yin layya.

Wani malamin addinin Musulunci, Muhammad Adewoyin ya gargadi Musulmi da su guji cin bashi don ganin son yanka abin layya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel