Murna Yayin da Malamin Musulunci da Aka Sace a Jihar Arewa Ya Shaki Iskar ’Yanci

Murna Yayin da Malamin Musulunci da Aka Sace a Jihar Arewa Ya Shaki Iskar ’Yanci

  • Rundunar ‘yan sanda a jihar Kogi ta tabbatar da kubutar babban malamin addinin Musulunci a jihar Kogi, Sheikh Quasim Musa
  • Kakakin rundunar a jihar, SP William Aya shi ya bayyana haka a yau Asabar 6 ga watan Afrilu ga manema labarai a birnin Lokoja
  • Wannan na zuwa ne bayan maharan sun sace malamin a ranar 25 ga watan Maris a garin Iyara da ke karamar hukumar Ijumu a jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi – Babban limamin masallaci a garin Iyara da ke karamar hukumar Ijumu a jihar Kogi ya shaki iskar ‘yanci daga hannun ‘yan bindiga.

Malamin mai suna Sheikh Quasim Musa ya yi nasarar fitowa daga kangin ne bayan sace shi da aka yi a ranar 25 ga watan Maris, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

PDP: Kungiyoyi sun ambaci Minista a cikin wadanda za a ladabtar saboda cin amana

Malamin Musulunci a jihar Arewa ya shaki iskar 'yanci daga hannun 'yan bindiga
Malamin Musulunci a jihar Kogi, Quasim Musa ya kubuta daga hannun 'yan bindiga. Hoto: Sheikh Quasim Musa.
Asali: Facebook

Sanarwar 'yan sanda game da malamin Musulunci

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, SP William Aya shi ya bayyana haka a yau Asabar 6 ga watan Afrilu, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aya ya bayyana haka ne ga manema labarai inda ya ce babban malamin ya shaki iskar ‘yanci bayan shafe kusan makwanni biyu.

“Ina mai sanar da ku cewa babban limamin masallacin Iyara, Alhaji Quasim Musa ya shaki iskar ‘yanci bayan garkuwa da shi.”

- William Aya

‘Yan bindiga sun farmaki dalibai mata

Har ila yau,a jihar Kogi, wasu mahara sun farmaki dakin kwanan dalibai a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke birnin Lokoja.

Maharan sun fasa dakin ne da tsakar dare inda suka shafe awanni biyu suna gudanar da aika-aika a cikin makarantar.

Wasu daga cikin daliban da abin ya shafa sun tabbatar da faruwar lamarin inda suka ce maharan sun kwashe musu kudi da wayoyi.

Kara karanta wannan

Neja: 'Yan bindiga sun kai hari kan masu ibada a lokacin sallar Tahajjud

‘Yan bindiga sun sace babban alamin Musulunci

A baya, mun kawo muku labarin cewa wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da babban limamin masallacin Juma’a a jihar Kogi.

Maharan sun sace Sheikh Quasim Musa ne a ranar 25 ga watan Maris a garin Iyara da ke karamar hukumar Ijumu a jihar.

Kafin sace malamin, maharan sun yi ta harbe-harbe tare da firgita mazauna yankin da saka su firgici a kokarin yin garkuwa da malamin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel