PDP: Kungiyoyi Sun Ambaci Minista a Cikin Wadanda Za a Ladabtar Saboda Cin Amana

PDP: Kungiyoyi Sun Ambaci Minista a Cikin Wadanda Za a Ladabtar Saboda Cin Amana

  • Rigimar cikin gidan da ta batawa jam’iyyar PDP lissafi a zaben shugaban kasar 2023 tana cigaba da ci da wuta har yau
  • Jam’iyyar adawar za ta yi zaman majalisar koli ta NEC, ana tunanin za a ladabtar da wadanda suka ci amanar PDP
  • Wasu kungiyoyi suna so a ladabtar da Nyesom Wike da sauran manyan da suka goyi bayan takarar Bola Tinubu a 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Har yanzu rikicin da ke tsakanin mutanen Atiku Abubakar da Nyesom Wike bai kare ba a babbar jam’iyyar hamayya ta PDP.

Ministan harkokin birnin tarayya da magoya bayansa sun yaki takarar Atiku Abubakar a zaben 2023, hakan ya kassara jam’iyyar.

Atiku Abubakar da Nyesom Wike
PDP: Ana so a hukunta su Nyesom Wike saboda yakar Atiku Abubakar Hoto: @Atiku, GovWike
Asali: Twitter

Wani rahoto da Punch ta fitar ya nuna har gobe bangarorin suna yaki da junansu domin ganin su ne ke rike da shugabancin PDP.

Kara karanta wannan

Ba a haka: Atiku ya taimakawa Tinubu da shawarwari kan karin kudin wutar lantarki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An dage sai PDP tayi taron NEC

Wannan tsama ta jawo aka hurowa majalisar Umar Damagum ta shirya taron NEC domin hukunta wadanda ake zargi da cin amana.

Ana zargin Nyesom Wike da mutanensa da aka fi sani da ‘yan G5 sun ci dunduniyar Atiku Abubakar da PDP a zaben shugaban kasa.

A makon da ya gabata NWC ta shirya za a yi zaman NEC a ranar 18 ga watan Afrilu an fara maganar a ladabta ‘ya ‘yan jam’iyyar.

Za a hukunta su Wike a PDP?

Kakakin PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya shaida cewa ba a gama yanke batutuwan da za a tattauna a wajen taron majalisar kolin ba.

Da aka tuntubi mataimakin shugaban matasa na kasa, Timothy Osadolor ya ce akwai bukatar shirya zaben shugabannin rassan jihohi.

Makomar 'yan G5 a jam'iyyar PDP

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya bayyana babban abin da yake tsoro gabanin Zaɓen da jam'iyya ta shirya

Rahoton Politics Digest ya nuna wadanda suka yaki Atiku Abubakar, suka goyi bayan APC a 2023 suna fuskantar barazana a jam'iyyar PDP.

Kungiyoyi masu zaman kansu sun rubutawa majalisar gudanarwa ta NWC takarda cewa a dauki mataki a kan irinsu Nyesom Wike.

Sauran sun hada da tsofaffin gwamnonin jihohin Enugu, Abia da kuma Benuwa, Ifeanyi Ugwuanyi, Okezie Ikpeazu da Samuel Ortom.

Wa zai zama sabon shugaban PDP?

Ana da labari wasu jagorori a PDP sun dage wajen ganin an samu wani daga Arewa maso tsakiya ya canji Dr. Iyorchia Ayu a NWC.

Manyan ‘yan siyasan da Legit Hausa take hangowa daga bangaren sun hada da Gabriel Suswam, David Mark da Bukola Saraki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel